Najeriya za ta mayar da ƴan gudun hijira fiye da 7000 gida daga Chadi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnatin Najeriya za ta mayar da ƴan ƙasar 7,790 da suka yi gudun hijra zuwa ƙasar Chadi da ƙungiyar Boko Haram ta tilastawa yin ƙaura shekaru fiye da 10 da suka gabata.

Babban mai taimaka wa gwamnan jihar Borno a fannin yaɗa labarai, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya naƙalto.

Sanarwar ta ce gwamna Umara Zulum ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Chadi bisa rakiyar ministan ma'aikatar jinƙai da yaye talauci, Yusuf Sununu tare da shugaban hukumar masu ƙaura ta ƙasar, Aliyu Ahmed.

Gwamna Zulum ya shaida cewa za a mayar da waɗanda suke da sha'awar komawa gida ne kawai.

"A kashin farko na mayar da mutanen, za a mayar da iyalai 1,768 da ke ƙunshe da mutum 7,790. Kamar yadda Zulum ya faɗi.

Yanzu da zaman lafiya ya samu a yankuna da dama na jihar Borno, a shirye muke mu tallafa wa mutanen da abin ya shafa wajen sake sada su da al'ummunsu." In ji gwamna Zulum.

Wata ƙididdigar hukumar masu ƙaura ta duniya, UNHCR ta nuna cewa akwai ƴan Najeriya da ke gudun hijra a Chadi fiye da 21,700 da kuma mutum fiye da 215,000 da yaƙin ya ɗaiɗaita.

Jihar Borno da Yobe da Adamawa ne dai jihohin da suka fi fuskantar rikicin mayaƙan Boko Haram da Najeriya ta kwashe shekaru fiye da 10 tana fama.