Bafalasɗiniyar da aka haifa bayan ɗaure mahaifinta ta yi arba da shi a karon farko

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Bayan jinkiri na sa'o'i da dama, farin ciki ya mamaye al'ummar birnin Ramallah, inda aka sako fursunonin Falasɗinawa kusan 60 da aka tsare a Isra'ila.

Daga ciki akwai wanda ya shaƙi 'yanci karon farko cikin shekara 22, Hussain Nassar mai shekara 47, wanda aka kama a shekara ta 2003 saboda ya taka rawa a boren Falasɗinawa na biyu (Intifada).

Daga cikin waɗanda suka zo tarbarsa akwai ƴaƴansa mata BIYU, Hedaya mai shekara 22 da Raghad, ƴar shekara 21. Dukansu suna sanye da riguna masu launin ja da baƙi, alamomin al'adar garinsu, Nablus.

Ƙaramar ta riga ta shaida mana cewa ba za ta iya kwatanta baƙin cikin da ta shiga ba a rayuwarta tsawon lokacin da ba da tare da mahaifinta.

"Wannan shi ne karo na farko da zan yi arba da shi, in taɓa shi, in kuma rungume shi, ba zan iya kwatanta yadda na ke ji ba."

Ta ce "Isra'ilawa sun kama shi lokacin da mahaifiyata ke ɗauke da ciki na. Ina ji kamar wannan ne karo na farko da zan san yadda ake samun uba!"

Daga cikin fursunonin Falasɗinawa 110 da aka sako a wannan mataki na tsagaita wuta akwai mata da ƙananan yara da dama - mai karancin shekaru a cikinsu shi ne mai shekara 15.

Wasu daga cikinsu ana zarginsu da ƙananan laifuka, wasu kuma ba a yanke musu hukunci ba ko kuma ba a tuhume su a hukumance ba.

Sai dai fursunoni 21 da aka samu da manyan laifuka da suka haɗa da kisan kai, Isra'ila ba ta ba su damar komawa gida zuwa yankin Falasdinu ba, sai dai aka kai su Masar ko kuma wasu ƙasashe maƙwabta.

Wani babban jigon da ba a tura shi gudun hijira ba, duk da hukuncin da aka yanke masa kan hannu a mutuwar wasu ƴan Isra'ila, shi ne Zakariyya Zubeidi.

Tsohon kwamandan rundunar Shahidai ta al-Aqsa na ɗaya daga cikin fursunoni da dama da magoya bayansa suka ɗaga shi sama suka kewaya da shi kan titunan da ke kusa da cibiyar al'umma ta Ramallah.

Lamarin ya kasance kamar yadda aka yi a baya inda ƙungiyar Hamas ta nuna ƙarfinta a Gaza wanda hakan na iya janyo wa wasu ƴan siyasan Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi su fara kiran ci gaba da yaƙi da Hamas a Gaza bayan wucewar wa'adin wannan matakin tsagaita wutar.

A ɓangaren gwamnar Ramallah da El Bireh, Dr Leila Abu Ghanam, wannan dawowa gida na tsoffin fursunonin da yawa wani lokaci ne na murna.

Sai dai tana ci gaba da samun tashin hankali yayin da ayyukan sojin Isra'ila ke ƙara tsananta a yankin arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, kuma har yanzu tsagaita wutar Gaza na tangal-tangal.

"Dukkan Falasɗinawa sun yi farin ciki da sakin fursunonin, amma muna baƙin ciki da abin da ke faruwa a larduna a daidai wannan lokaci. Iyaye mata a yau duk da irin murnar da suke yi na sakin ƴaƴansu, suna taya iyayen da suka rasa gidajensu da ƴaƴansu baƙin cikin wannan rashi".

A yau na ɗaya ne daga cikin kwanaki ƙalilan da tun lokacin da na fara bibiyar wannan rikici mai wuyar warwarewa, da na ga fuskoki da yawa cike da farin ciki a ɓangaren Falasɗinawa da Isra'ilawa.

Ya kasance mummunan yaƙi wanda ya lalata rayuka da dama.

Gwamna Ghanam ta zargi gwamnatin Isra'ila da rashin son zaman lafiya. "Amma ba za mu cire rai ba" ta faɗa yayin da ta ke murmushi. "Idan da mun yi ƙasa a gwiwa, da Falasɗinawa sun ƙare shekara 75 da suka wuce."

Ana sa ran sako rukunin fursunoni na gaba da za a yi musaya da Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su ranar Asabar.