Rodri ya fara atisaye a Man City

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da Ballon d'Or, Rodri ya fara atisaye a Manchester City.
Ranar Juma'a ɗan wasan tawagar Sifaniya ya motsa jiki shi kaɗai a filin atisayen Manchester City.
Rodri mai shekara 28, ya fara jinya tun cikin Satumba, bayan da ya ji rauni a gwiwa.
Ya ci karo da cikas a wasan da City ta tashi 2-2 da Arsenal a Premier ranar 22 ga watan Satumba, Erling Haaland da John Stones ne suka ci wa City ƙwallayen.
Yayin da Riccardo Calafiori da kuma Gabriel Magalhaes suka ci wa Gunners nata ƙwallayen.
Wasa uku ya buga a bana da ya haɗa da biyu a Premier League da ɗaya a Champions League, shi ne wanda aka tashi 0-0 tsakanin City da Inter Milan cikin Satumba.
Kafin nan ya buga karawar da City ta doke Brentford 2-1 a Premier League ranar 14 ga watan Satumba.
Rashin Rodri ya sa City tana ta huɗun teburi da tazarar maki 20 tsakani da Liverpool mai jan ragama, bayan da ƙungiyar Etihad ce ke rike da kofin bara.
Haka kuma Real Madrid ta yi waje da City a Champions League a wasan neman cike gurbin shiga zagayen ƴan 16.
Tun farko an ce Rodri ya kammala buga wasannin bana, amma City ta saka hoton ɗan wasan yana atisaye ranar Juma'a.
Pep Guardiola ya yi watsi da batun cewar Rodri na daf da komawa buga wa City wasannin da suka rage a kakar nan.
City ta saka sunan Rodri cikin ƴan wasan da za su buga mata Champions League tun cikin Fabrairu, koda yake an yi waje da ƙungiyar daga gasar bana.












