Labarin matashin da ya tsallake rijiya da baya da iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Labarin matashin da ya tsallake rijiya da baya da iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi
An wallafa

Abubakar Shehu ɗaya ne daga cikin mafarautan da suka kuɓuta a harin, ya kuma bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya daga harin masu ɗaukar doka a hannun.

Ya ce wannan ne karonsa na farko da ya je farauta a Fatakwal, kuma a lokacin da suka isa Uromi, ƴan sintiri sun tare su.

"A lokacin da muka isa Uromi, sun tare mu a kan titi, suka ce mu sauko daga cikin mota.''

Baya ga Abubakar, BBC ta kuma ji daga bakin wasu iyalai mata na waɗanda aka kashe ɗin.