Jam'iyyar APC na gab da samun gagarumin rinjaye a majalisar ƙasar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Larabar nan ne ƴan majalisar dattawa guda huɗu da na wakilai guda uku suka sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa mai mulki ta APC.

Ƴan majalisar sun bayyana dalilansu na sauya sheƙar da suka haɗa da rikicin cikin gida da rashin aƙida da rashin tabbas da jam'iyyar ta hamayya ke fama da su.

Wannan dai wani mataki ne da masu nazarin kimiyyar siyasa ke kallo da zai sa jam'iyyar APC mai mulki ta samu gagarumin rinjaye a zaurukan majalisun biyu ta yadda jam'iyyar za ta rinƙa amince wa da buƙatun ɓangaren zartarwa ba tare da samun tirjiya daga jam'iyyun hamayya ba.

Sauya sheƙa a Majalisar Dattawa

Sanatocin da suka sauya sheƙar zuwa APC daga PDP sun haɗa da Francis Fadahunsi daga Osun ta Gabas da Oluwale Olubiyi daga Tsakiyar Osun da Aniekan Bassey na mazaɓar arewa maso gabashin jihar Akwa Ibom da kuma Samson Ekong daga Kudancin jihar Akwa Ibom.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yayin da yake karanta takardun da ƴan majalisar suka aika wa majalisar kan dalilansu na ficewa daga jam'iyyar ta PDP, ya ce rashin tsari da daidaito ne ya tilasta ƴan majalisar ficewa daga jam'iyyar.

Ga jadawalin yawan ƴan majalisar dattawan da jam'iyyu ke da su a yanzu:

  • APC 70
  • PDP 28
  • Labour Party 5
  • NNPP 1
  • SDP 2
  • APGA 1

Abin da hakan ke nufi shi ne daga cikin ƴan majalisar dattawan ƙasar 109, jam'iyyar APC mai mulki na da mafi yawan sanatocin inda a yanzu haka kujeru uku kawai suka rage mata ta samu gagarumin rinjayen da za ta iya zartar da al'amuran majalisa ba tare da buƙatar goyon bayan jam'iyyun hamayya ba.

Jadawalin yawan sanatoci ga jam'iyyu a Yunin 2023:

  • APC 59
  • PDP 36
  • Labour Party 8
  • SDP 2
  • NNPP 2
  • APGA 1
  • YPP 1

Jadawalin Sanatocin da suka sauya sheƙa zuwa APC kafin yanzu:

  • Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba daga Sokoto - PDP zuwa APC
  • Sanata Ifeanyi Ubah YPP zuwa APC, kafin rasuwarsa.
  • Sanata Ned Munir Nwoko daga jihar Delta ya bar PDP zuwa APC.
  • Sanata Ezenwa Onyewuchi daga jihar Imo daga LP zuwa APC.
  • Sanata Kawu Sumaila daga jihar Kano ya daga NNPP zuwa APC.
  • Sanata Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya)
  • Sanata Yahaya Abdullahi (Arewacin Kebbi)
  • Sanata Garba Maidoki (kudancin Kebbi)

Sauya sheƙa a Majalisar Wakilai

A majalisar wakilai kamar takwararta da dattijai, a ranar Larabar ƴan majalisar uku ne suka sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki.

Ƴan majalisar wakilan da suka sauya sheƙa su ne a ranar Laraba:

  • Hon. Ajilesoro Taofeek Abimbola daga jihar Osun
  • Hon. Omirin Olusanya daga jihar Osun
  • Hon. Marcus Onobu daga jihar Edo

Dangane da dalilansu na ficewa daga PDP, shugaban majalisar wakilan, Tajuddeen Abbas yayin da yake karanta wasiƙunsu ga zauren majalisar ya ce sun bar PDP saboda rikicin cikin gida da rashin tabbas da suka baibaye jam'iyyar.

Jadawalin ƴan majalisar da suka koma APC kafin yanzu:

  • Hon, Idris Sulaiman Abubakar daga jihar Kogi - ADC zuwa APC.
  • Hon. Chris Nkwonta daga Abia -PDP zuwa APC.
  • Hon. Sulaiman Abubakar daga Zamfara - PDP zuwa APC
  • Hon. Chinedu Okere daga Imo,
  • Hon. Mathew Donatus daga Kaduna
  • Hon Bassey Akiba daga jihar Ribas
  • Hon. Esosa Iyawe daga jihar Edo.
  • Alfred Ajang daga Plateau
  • Hon. Amos Magaji daga Kaduna
  • Hon. Garba Koko daga Kebbi
  • Ƴanmajalisar wakilai shida daga jihar Delta
  • Hon Kabiru Usman daga Kano - NNPP zuwa APC
  • Hon Abdullahi Sani - NNPP zuwa APC

Jadawalin yawan kujeru ga jam'iyyu a majalisar wakilai a 2023:

  • APC 162
  • PDP 102
  • LP 34
  • NNPP 18
  • APGA 4
  • ADC 2
  • SDP 2
  • YPP 1

A yanzu haka ƙididdiga ta nuna cewa jam'iyyar APC mai mulki na da ƴan majalisar wakilai 210, inda ta samu ƙarin ƴan majalisa 48 sakamakon sauya sheƙa daga jam'iyyun hamayya musamman babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Kuma hakan na nuni da cewa akwai yiwuwar jam'iyyar APC ka iya samu gagarumin rinjaye na 240 na baki ɗaya ƴan majalisar wakilan 360, wani abun da zai bai wa jam'iyyar damar amince wa da buƙatun ɓangaren zartarwa ba tare da samun cikas ba.

'Sauya sheƙar na ƙara wa Tinubu goyon baya a majalisa'

Dakta Kabiru Sa'id Sufi, malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke Kano ya ce sauya sheƙar na ƙara yawan ƴan jam'iyyar shugaban ƙasa, wato Bola Tinubu a majalisar tarayya.

"Hakan na nuwa cewa Tinubu da jam'iyyarsa na ƙara samun goyon baya. Kuma duk wani ƙuduri da zai zo daga wajensa zai samu sahalewar majalisa cikin sauƙi.

"Su ma a majalisa duk ƙuduri da zai fito daga wajensu, zai kasance wanda yake daɗaɗa wa shugaban ƙasa da jam'iyyarsa. Hakan zai sa ƙarfin adawa da gwamnatinsa a majalisa ya ragu," in ji Dakta Sufi.

Sai dai ya ce hamayya tana da muhimmanci a majalisa kuma a majalisa ne ya kamata ta fi taka rawa saboda nan ne ake bijiro da ayyukan raya ƙasa da wanda zai iya daɗaɗawa ko cutar da al'umma.

Ya ce idan ya kasance kullum ƴan ƙasa na rasa muryarsu a majalisa, to kamar ana raunata muryar al'umma ne musamman idan aka bijiro wani abu da ba shi da alfanu da al'umma.

Illar sauya sheƙa a majalisa

Dakta Kabiru Sufi ya bayyana cewa batun sauya sheƙa da ƴan majalisar ke yi, zai rage ƙarfin dimokraɗiyya da kuma karsashinta.

"Adawa a dimokaɗiyya kamar gishiri ne a miya. Wani lokaci wanda yake mulki na buƙatar muryoyin abokan adawa domin su gyara masa kura-kuransa da ɗora shi kan turba mai yau, musamman idan aka bijiro abin da zai cutar da ƴan ƙasa.

"To idan dimokraɗiyya ta rasa wannan abin ba zai zama alfanu mai kyau ba, kuma ta rasa wani jigo," in ji Dakta Sufi.

Ya ce barazanar da hakan zai yi shi ne mayar da majalisa ƴan amshin shata, inda ba su dubi abubuwa cikin tsanaki ba.

"Duk lokacin da aka ce babu ƙwaƙwarar adawa a majalisa zai kasance ɓangaren mai mulki yana yin abin da ya ga dama, kuma ba lallai ya kasance abu ne da aka yi don al'umma ba," in ji shi.

Ya ce abin da ya kamata a yi shi ne su ma ɓangaren hamayya su laluɓo abin da ya za su yi don dakatar da hakan.

"Tun da sauya sheƙar na ta faruwa, ya kamata ƴa adawa su tsaya don ganin sun samar da fita kan haka da kuma ganin sun dawo da mutanen su da suka rasa," in ji Dakta Kabiru Sufi.