Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin 'gaba kura baya sayaki' da rikicin ƴan aware da sojoji ya jefa al'umma a Kamaru
- Marubuci, Nick Ericsson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ngabi Dora Tue na cikin matuƙar baƙin ciki abin da ya sa ta fama da rayuwa.
An ajiye akwatin gawar mijinta Johnson Mabia a tsakiyar masu juyayi da suka yi dandazo a garin Limbe da ke yakin kudancin Kamaru - wanda a baya ya sha fama da irin wannan yanayi na baƙin ciki.
'Yan aware ne dai masau ɗauke da makamai suka kama Johnson - wanda ma'aikacin gwamnati ne da ke yankin renon Ingilishi - a lokacin da sule kan hanyar zuwa wurin aiki tare da wasu abokan aikinsa biyar.
Waɗannan 'yan tawayen ar yanzu suna ci gaba da yaƙin neman 'yancin yankunan reon Faransa biyu na Kamaru. Yaƙin da aka kwashe kusan shekaru goma ana fafatawa da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da jefa jama'ar yankin cikin tashin hankali.
Laokacin da aka kama shi kimanin shekara huɗu da suka gabata, Dora ta yi ƙoƙarin samun ganin Johnson, amma kuma 'yan awaren sun saka mata kuɗin fansa da yawansu ya kai fam 55,000 da suka nemi a biya cikin sa'a 24 domin a sake shi. A lokaci guda kuma ta samu kiran waya daga wani ɗan'uwan Johnson.
"Ya ce…in kula da yara. An kashe mijina. A wannan lokacin ban ma san me zan yi ba. Ranar Talata ne tafiyar ta kama shi, kuma aka yi garkuwa da shi. Aka kashe shi a ranar Jumu'a" in ji Dora.
Wani maras daɗi ma shi ne 'yan awaren sai da suka daddatsa gawar Johnson kafin daga bisani su jefar da ita a gefen hanya.
Tushen rikicin na 'yan awaren ya soma ne tun daga loacin da ƙasar ta samu 'yancin kanta a 1961 da kuma kafuwar yankin renon turawan Ingilish a shekarar 1972 da zama takwaran yankin reno turan Faransa.
Tun a lokacin masu amfani da harshen Turancin Ingilshi suka soma jin ba a yi musu daidai ba ganin kamar gwamnatin ƙasar ta ware su . Johnson dai rikicin ya auka masa ne da tsakar rana har ya gamu da kisan na gilla amma ba ya daga cikin kowane ɓangare na masu tayar da ƙayar baya.
A farkon shekarar 2016, aka soma wata zanga-zangar lumana akan abin da suka bayyana da yawan amfani da tsarin shari'a na Faransa a kotunan ƙasar. Lardunan biyu da ke ƙarƙashin ikon Ingilishi da Faransa na amfani da tsarin shari'a daban-daban.
Daga bisani zanga-zangar ta watsu har ta kai aka soma rufe kantuna da makarantu.
Sannan gwamnatin ƙasar ta ɗauki tsattsauran matakin gaggawa - ida aka yi ta dukan mutane, tare da kama jama'a masu ɗimbin yawa. Abin da Ƙungiyar Ƙasashen Afirka suka kira da "amfani da ƙarfin da ya wuce kima".
To sai dai ma'akatar tsaron Kamaru ba ta ce kome akan wannan batun da ma wasu ba.
Sai kuma aka samu ɓullar gungun masu dauke da makamai. Sannan a ƙarshen shekarar 2017 rikicin ya ci gaba da yaɗuwa, inda shugabannin 'yan awaren ɓangaren renon Faransa suka bayyana kafa ƙara da suka kira Jamhuriyar Ambazoniya.
Zuwa yanzu an an jefa mutum milyan biyar 'yan Kamaru da ke yankin renon Ingilishi cikin rikici, kwatankwacin kashi biyar cikin ɗari na dukan yawan jama'ar ƙasar. An kashe aƙalla mutum 6,000 kana an tilasawa dubban ɗaruruwa barin gidajensu.
"Za ka ta shi ka tashi da safe ka ga gawarwakin ko'ina warwatse akan hanyoyi," inji Balise Eyong, wani ɗan jarida daga Kumba na yakin renon turawan Ingilshi da ke kudancin ƙasar, wanda kuma ya taɓa yi wa BBC Eye wani shiri na ilmantarwa akan rikicin, shi ma dai a shekarar 2019 an tilasta masa barin gidansa tare da iyalansa.
"Ko kuma ka ji an ce an cinnawa gida wuta. Ko ka ji an ce an sace wani. An yi gunduwa-gunduwa da sassan jikin mutum. To, ta ya za ka zauna a garin da kullum safiya kana fargabar me zai faru da 'yan uwanka?"
Gwamnatin ƙasar tare da ƙasashen duniya da dama sun sha ƙoƙarin sassanta rikicin, ciki har da abin da gwamnatin ta kira "babbar tattaunawar sassantawa" a sheakarar 2019.
Abu guda ne aka cimma a yayin tattaunawar shi ne sassan biyu sun amince da tarihin samuwar juna, baya gare shi ba a cimma takaimaiman sulhu ba.
Felix Agbor Nkongho - lauya ne wanda yana ɗaya daga cikin jagororin zanga-zangar 2016 wanda daga baya aka kama shi - ya ce ɓangarorin biyu a yanzu na zaune ne kara zube.
Ya shaidawa BBC Eye cewa "Akwai lokacin da ....idan mutane na neman samun natsuwa da tsaro su kan koma ɓangare 'yan aware".
"Amma shekaru biyu da suka gabata, ban yi tsammanin akwai wani mutum mai natsuwa da zai yi tunanin 'ya aware na da hanyar samar masa da kariya ba. Kan haka, ya kamata kowa ya kasance tare da mu domin samun 'yanci, kuma tambayar da na kan yi ita ce: wanene za ka mulka?"
Amma ba 'yan aware ne kaɗai aka zarga da laifukan ci zarafi ba.
Ƙungiyoyi irin na Kare Hakkin Ɗan'adam su tattara bayanai kan cin zarafin da jami'an tsaro suka suka yi wa masu fafutukar samar da ƙasar renon Faransa. Sun samu bayanan ƙona ƙauyuka da zabtarwa, tare da tsare mutane ba bisa ƙaida ba da kuma kisan ba gaira ba dalili, wanda galibi saura al'ummar duniya ba su san da su ba.
Misalan azabtarwa da gwamnati ta ɗauki nauyi ba a ɓoye su ke ba.
John (ba wannan ne sunansa na gaskiya ba) dakarun sojin Kamaru ne suka ɗauke shi, inda suka zarge shi da yin safarar makamai ga 'yan aware.
Johan ya tuna cewa bayan an tsare shi ne sai aka miƙa musu wasu takardu aka nemi su saka hannu ba tare da ba su damar karanta bayanan da ke ciki ba, da suka yi ynƙurin kaucewa hakan sai aka soma azabtar da su.
Amma fa wannan ba gaskiya ne ba.
Wata daya da kama shi, sai aka saka wani mutum a ɗaki guda da shi, wanda ya sanar da shi cewa abokinsa ya mutu a ɗakin da aka tsare shi ana azabtar da shi. Wata ɗaya sai aka saki John ba tare da an tuhume shi ba.
John ya ce, "Na zauna cikin fargaba saboda ban san ta ina ma zan fara ba ko ina ya fi sauƙi in fara ko ma ta ya zan fara".
A watan Oktoban 2020, an kaiwa wata makaranta a Kumba hari. Babu wanda aka zarga da kai harin amma gwaati ta ɗora alhakin haka akan 'yan awaren. Wasu mutane dauke da adduna da bindigogi kuma sun kashe aƙalla yara bakwai.
Lamarin ya ya jawo suka da Allah-wadai daga al'ummar duniya.
"Kusan rabin makarantun yankin aka rufe" a cewa ɗan jarida Eyong.
Bayan duk waɗannan rikice-rikicen da suka faru tsakanin gwamnati da 'yan aware daban-daban, an sake samun wasu 'yan tawaye da suka ɓulla a yankin 'yan awaren domin su yaƙi 'yan Amabazoniya a wani matakin sake ha ƙasar.
Jagoran ɗaya daga waɗannan kungiyoyi, mai suna John Ewome (wanda aka fi sani da Moja Moja) ya kan jagoranci sintiri akai-akai agarin Buea domin neman 'yan aware har zuwa lokacin da shi kuma aka kama shi a watan Mayun 2024.
Shi ma dai a zarge shi da take hakkin bil'adama da cin zarafi tare da azabtar da waɗanda ba su ɗauke da makamai da ake dangantawa da masu goyon bayan 'yan aware ne. Sai dai ya musanta zarge-zargen. "Ban taɓa ɗora hannuna akan duk wani farar hula ba, kawai sai 'yan Ambazoniya, kuma ina rantsuwa gaskiyata za ta fisshe ni," ya shaidawa BBC.
Baya ga haka, aka ci gaba da sace mutae tare da kisan su.
An tura shi cikin daji tare da wasu mutum 15 waɗanda aka kashe biyu a cikin su a gaban idonsa. Sai dai an sake shi a lokacin da sojoji suka kama sansanin.
Bayan shekara biyu da yin jan'izarsa sai aka sake samun labarin cewa an ga gawaqr abokansa biyar da aka yi garkuwa da su tare.
Akwai dai ƙarin iyalai da a yanzu suke fama da gagarumar hasarar hasarar 'yan'uwansu da suka yi. Ga Ngabi Dora Tue wadda ke zaune rungume da jaririnta tana ganin rayuwarta za ta faɗa cikin ƙunci
"Ina da ɗimbin bashi da dole in biya, ban kuma san yadda zan iya haka ba," in ji ta.
"Na yi tunanin in shiga karuwanci don in samu kuɗi, amma ina gudun abin kunyar da hakan zai jawo min. Kan haka na daure in ci gaba da tafiya a haka. Na rasa mijina tun ina da ƙurciya."
BBC ta nemi ƙarin bayani daga Dakarun Sojojin Ambazoniya (ADF), wadda ke iƙirarin ita ce rundunar 'yan aware mafi girma.
Amsar da ta bayar ita ce akwai kunhgiyoyin mayaƙan 'yan aware da dama da ke zaune a yankin renon Faransa.
Rundunar ta ADF ta ce tana aiki ne bisa dokokin ƙasa da kasa kuma ba ta kai ma ma'aikatan gwamnati da makarantu da 'yan jarida da fararen hula hari.
A maimakon haka ma ta zargi wasu mutanen da ta ce suna kai hare-hare ne ba da sunan ADF ba.
Ƙungiyar ta kuma zargi wasu a gwamnati da aikata ta'asa yayin da suke iƙirarin su mayaƙan Ambazoniya ne da ke son mayar da al'ummar yankin akan fafutukar ƙwatar 'yanci..