Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Man City za ta kai kwata fainal a Champions League?
Manchester City za ta kara da RB Leipzig a wasa na biyu zagayen 'yan 16 a Champions League ranar Talata a Etihad.
Sun tashi 1-1 a karawar farko a bana a Jamus, Riyad Mahrez ne ya fara ci wa City kwallo a bugun fenariti, daga baya Josko Gvardiol ya farke.
Wannnan shine wasa na hudu da za su kece raini a tsakaninsu, City ta yi nasara a daya da canajaras daya, sannan Lepzig ta ci wasa daya.
Leipzig za ta buga wasan ba tare da Xaver Schlager da kuma Christopher Nkunku, wadanda ke jinya.
Sun ji rauni a wasan Bundesliga da suka yi tata burza da Borussia Dortmund.
Kungiyar da Marco Rose ke jan ragama, wadda take ta uku a teburin Bundesliga ta yi rashin nasara wasa biyu a dukkan fafatawa tun daga watan Satumba.
City wadda ke rike da Premier League na bara tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal ta daya.
Wasa uku da suka kara a tsakaninsu:
2022/2023 Champions League
- RB Leipzig 1 - 1 Man City
2021/2022 Champions League
- RB Leipzig 2 - 1 Man City
- Man City 6 - 3 RB Leipzig
Akwai karin bayanai......