Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wani wawakeken rami mai ban al’ajabi ya bayyana a Chile
Wani wawakeken rami mai ban al’ajabi ya bayyana a Chile
An wallafa
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Hukumomi a ƙasar Chile suna bincike kan wani rami da ba a san da shi ba da ya bayyana a ƙarshen makon jiya.
Ramin ya bayyana ne a wani yanki da ake haƙar ma’adinai a arewacin ƙasar.
Wani bidiyo ya nuna wawakeken ramin a wajen da kamfanin haƙa na Canada mai suna Lundin Mining ke aiki.
Hukumar kula da haƙar ma’adinai ta ƙasar, Sernageomin, ta aika tawagar ƙwararru yankin, wanda ke da nisan kilomita 665 daga Santiago, babban birnin ƙasar.