Ranar Malamai ta Duniya: Mutumin da yake sadaukar da kashi 80 na albashinsa wajen koyar da marayu

Bayanan bidiyo, Mutumin da yake sadaukar da kaso 80 na albashinsa wajen koyar da marayu
Ranar Malamai ta Duniya: Mutumin da yake sadaukar da kashi 80 na albashinsa wajen koyar da marayu
An wallafa

Tijjani Mukaddas Hadejia, mai karatun digiri na uku, ya kafa makarantar sha-ka-tafi a unguwar Dakwa da ke Abuja inda yake koya wa yara marayu da marasa galihu.

Malam Tijjani ya ce ya sadaukar da kashi 80 na albashinsa wajen daukar nauyin yaran da suke makaranta .

“Muna daukar yara hazikai daga cikinsu mu sanya su a makarantun da suka dace da karatunsu. Muna sanya wasu a firamare ko sakandare ko ma jami’a," in ji shi.

Ya ce dalilin da y asa ya kirkiro wannan makaranta shi ne yadda y aga kananan yara marasa galihu na neman fada wa yanayin da rayuwarsu ba za ta yi kyau a gaba ba.

"Wasu a cikinsu talla suke yi. Wasu kuma yawon banza suke yi.”

Malam Tijjani Mukaddas dai ya zama wani abin kwatance a tsakanin al.’ummar yankin Dakwa musamman talakawa bisa gudunmowar da yake bayarwa ta fannin ilimi.