Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Liverpool Alisson da Jota za suyi jinya
Mai tsaron ragar Liverpool, Alisson da Diogo Jota, za su yi jinya, bayan raunin da suka ji a gasar Premier League ranar Asabar.
Liverpool ta je ta tashi 1-1 da Manchester City a wasan mako na 13 a babbar gasar tamauta ta Ingila.
Kociya, Jurgen Klopp ya ce raunin Alisson ba wani mai muni ba ne, amma zai ji jinyar mako biyu, ba a sanar da ranar da Jota zai koma taka leda ba.
Jota, dan kasar Portugal ya hakura da wasan a minti na 54 a Etihad, shi kuwa Alisson da shi aka karasa fafatawar.
Liverpool za ta karbi bakuncin LASK a Europa League ranar Alhamis, daga nan za ta fafata da Fulham a Premier League ranar Lahadi.
Daga nan kungiyar Anfield za ta kai ziyara Sheffield United ta kuma fafata da Crystal Palace a Premier League.
Daga nan za ta fuskanci Union St Gilloise a Europa League, sannan ta karbi bakuncin Manchester United a Anfield ranar 17 ga watan Disamba.