Bellingham ya zama matashin ɗan ƙwallon da ya fi ƙoƙari

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Ɗan wasan tsakiya na Ingila da Real Madrid Jude Bellingham ya lashe kyautar 'Golden Boy' na 2023 - wanda aka bai wa gwarzon ɗan wasan ƙasa da shekara 21 a manyan gasannin Turai.
Ƴar wasan gaban Colombia da Real Madrid Linda Caicedo, mai shekara 18, ta lashe kyautar ta mata.
Bellingham, mai shekara 20, ya koma Real ne daga Borussia Dortmund a bazara kuma ya ci ƙwallaye 13 a wasanni 14 da ya buga.
Wannan lambar yabo ta zo ne bayan da aka karrama shi a matsayin ɗan wasan ƙasa da shekara 21 wanda ya fi hazaƙa a duniya a bukin Ballon d’Or da aka yi a watan Oktoba.
Bellingham shi ne ɗan wasan Ingila na farko da ya lashe kyautar tun bayan Raheem Sterling a shekarar 2014, lokacin da ɗan wasan na Chelsea ya ke Liverpool.





