'Babban hadari ne rashin tsugunar da 'yan Boko Haram da suka mika wuya'

An wallafa

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun ce akwai babban hadari idan har 'yan kungiyar Boko Haram din da suka mika wuya suka rasa matsugunni.

 

Masanan sun yi tsokacin ne bayan da hukumomi a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, suka ce ana fama da karancin wurin ajiye dubban 'yan kungiyar ta Boko Haram da suka mika wuya.

 

Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi ne kan lamurran tsaro, ya shaida wa BBC cewa akwai hadarin gaske idan har gwamnati ko hukumomin tsaro suka gaza wajen samar da matsugunnai ga wadannan ‘yan Boko Haram din.

 

"Babban hadarin shi ne za su iya kubucewa su koma in da suka fito wato kungiyarsu, saboda da yawa daga cikinsu yunwa ko rashin yarda da wani abu a kungiyar ne ya sa suke fita daga kungiyar su mika wuya."

 

Masanin tsaron ya ce idan har suka je sansanin suka ga babu abincin da za a ci a koshi sannan rayuwa ta ki dadi a wajen, ko kuma duk da sun mika wuya an ki yi musu abin da ya dace misali na rashin mayar da su cikin al’umma, to babban abin da za su fara yi shi ne su gudu su koma kungiyarsu.

Barista Bukarti, ya ce "Abu na biyu za su iya wanke kan wasu wadanda su ba ‘yan kungiyar ta Boko Haram ba ne sun kuma hadu da su a irin zaman sansani, sai su wanke su don su koma kungiyar tasu."

 

Ya ce abu na uku tun da ita kungiyar Boko Haram din na jin haushin wadanda suka mika wuyan, to za ta iya kitsa hari ta kai irin wuraren da aka ajiye su don ta kashe su.

 

Masanin tsaron ya ce dole idan gwamnati na son kare duk abubuwan da ya lissafa, to na farko shi ne gwamnati ta fito ta fada wa mutane gaskiya a kan matsayin mutanen da suka mika wuyan.

 

Ya ce,” Abu na biyu shi ne gwamnati ta yi tsari mai kyau tun da dai za a ci gaba da samun irin wadannan mutanen da za su rinka mika wuya.”

 

Barista Bukarti, ya ce dole sai gwamnati ta smaar da isassun sansanoni na ajiye irin wadannan mutane da kuma isassun kayan kula da su ciki har da tsare su daga hare-hare, da tabbatar da cewa ba su koma kungiyar ba.

Karin bayani

Kwamandan rundunar yaki da matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya, wadda ake kira ''Operation Hadin Kai'', Manjo Janar Chris Musa, ya ce ya zuwa yanzu tsofaffin 'yan kungiyar kusan dubu sittin da bakwai (67,000) ne suke jiran a karbe su.

 

Sai dai wurin da ake da shi ba zai dauke su ba.