Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Golan Real, Courtois ya cika shekara 31 da haihuwa
Golan Real Madrid, Thibaut Courtois yana bikin cikarsa shekara 31 da haihuwa ranar Alhamis, wanda yake kaka ta biyar a Santiago Bernabeu.
An haifi Courtois ranar 11 ga watan Mayun 1992, wanda ke tsare ragar tawagar kwallon kafa ta Belgium.
Courtois ya fara yi wa Real Madrid tamaula ranar 1 ga watan Satumbar 2018 a fafatawa da Leganes a Bernabeu, kawo yanzu ya tsare ragar Real sau 224.
Golan ya lashe kofuna da yawa a kungiyar Sifaniya ciki har da Champions League da Club World Cups biyu da European Super Cup.
Tsohon dan wasan Chelsea ya dauki LaLiga biyu da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cups biyu a Real Madrid.
Rawar da mai tsaron ragar ke takawa a Real Marid ta sa ya lashe kyautar kofin Yashin a 2022 da kuma na Zamora a 2019/20.