Tseren kekuna da bikin al`adun kabilar Maasai a cikin hotunan Afirka

fd

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kwararren ɗan tseren kekuna Welay Hagos Berhe yayin gasar Tour de Suisse ranar Lahadi a Switzerland.
An wallafa
w

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin magoya bayan Biniam Girmay ɗan kasar Eritrea su na farin cikin nasarar da ya yi a zagaye na biyu na tseren kekunan.
a

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yan wasan kokawa Spar da Tumble yayin da suke fafata kokawar jiu-jitsu ta Braziliya a birnin Nairobi na kasar Kenya.
ds

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin matashiya yar shekaru 17 ta na karbar horo a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu, a filin makarantar koyar da wasan kwallon kwando da tauraron kwallon kwando Luol Deng ya gina.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mata su na rera wakar gargajiya a lokacin bikin al`adun gargajiya na Maasai a Kenya a ranar Asabar.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shekarar farko ta bikin, wanda ake gudanarwa a garin Sekenani wanda ke dajin Maasai Mara.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Manufar bikin ita ce nuna al`adun gargajiya da kayan adon kabilar.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata Zabiya ta na taimakawa a ayyukan gida tare da yan`uwanta a Dakar Babban birnin kasar Sinigal, a ranar Talata wacce ke zama ranar wayar da kai game da zabiya a duniya.