Amsar tambaya 10 kan batun binne Sarauniya

An wallafa

Mutuwar Sarauniya Elizabeth II ta yi babban tasiri ga rayukan al'ummar Birtaniya. Gwamnati ta ce za a ci gaba da zaman makokin rasuwarta a hukumance har zuwa karshen ranar da za a binne ta.

Yaushe ne za a binne Sarauniyar?

Hidundimun binne Sarauniyar za su auku ne da misalin karfe 11 na rana ranar Litinn 19 ga watan Satumba. Za a gudanar da wannan muhimmin aikin ne a cocin Westminster Abbey - wanda coci ne mai cike da tarihi domin a nan ne ake bikin nada sarakunan Birtaniya.

Me ake nufi da bikin binne sarki a hukumance?

A kan yi wasu hidundimu a hukumance, bikin da ake bin wasu tsare-tsare na musamman.

Akan fara da wani faretin soji tare da sojoji dauke da gawar basaraken da ya mutu zuwa wani daki mai suna Westminster Hall, wurin da ake ajiye gawar domin masu ziyara su yi ta'aziyyarsu.

Daga nan sai a gabatar da wasu addu'o'i a cocin Westminster Abbey ko a cocin St Paul's Cathedaral.

Sai dai ba kasafai akan yi wa wani babban mutum irin wannan hidimar ba bayan ya mutu.

Cikin wadanda aka ba irin wannan karramawar bayan mutuwarsu akwai Sir Isaac Newton da Lord Nelson da kuma LOrd Palmerston.

Irin wannan karramawar ta karshe da aka yi ta marigayi Sir Winston Churchill tsohon firaministan Birtaniya, wanda aka yi ranar 15 ga watan Fabrairun 1952.

An kuma yi wa wasu fitattun 'yan Birtaniya irin wannan karramawar bayan mutuwarsu, ciki har da wadda aka yi wa Diana, Gimbiyar Wales a 1997 da ta mahaifiyar Sarauniya wato Elizabeth a 2002. Sai kuma karrmawar da aka yi wa Baroness Margaret Thatcher - tsohuwar firaministar Birtaniya - wadda a ka binne a cocin St Paul Cathedral a 2013.

Su waye za su halarci binne Sarauniya?

Kawo yanzu ba a wallafa sunayen manyan bakin da za su halarci binne Sarauniya Elizabeth ba.

Sai dai ana sa ran shugabanni da sarakuna da 'yan gidan sarauta daga kasashen duniya za su shiga sahun 'yan gidan sarauntar Birtaniya a ranar da za a binne ta.

Kawo yanzu, Fadar White House ta sanar cewa Shugaban Amurka Joe Biden zai halarci binnewar, inda ita ma firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta sanar za ta tafi Birtaniya domin binnewar.

Me ajiye gawa a cocin Westminster Hall ke nufi?

Cikin wani lokaci mai tsawon sa'a 24 daga tsakiyar yinin Litinin, za a ajiye gawar Sarauniya a cocin St Giles da ke birnin Edinburgh.

Al'ummar birnin na iya zuwa domin mika ta'aziyyarsu da karrama ta.

A ranar Laraba kuma, za a fara irin wannan karramawar a Westminster Hall da misalin karfe 5 na yamma agogon Birtaniya har zuwa kashegari.

A kan ajiye gawa a bainar jama'a ne kafin lokacin da za binne ta.

A kan yi irin wannan karramawar ga sarki ko sarauniya ko matar sarki, da kuma a wani lokacin a kan karrama tsofaffin firaministoci.

Ana sa rai dubban darurruwan mutane za su halarci wurin da aka ajiye gawar inda za su yi dogayen layuka domin bi ta kusa da akwatin gawar Sarauniyar.

Mene ne 'kwana ana yi wa gawar Sarauniya addu'o'i?'

Lokacin da ake dauka domin kula da gawar da aka ajiye, ana amfani da shi ne domin yi ma Sarauniyar addu'o'i.

A ranar Litinin, ana sa ran Sarki Charles III zai dauki lokaci yana yin addu'o'i a gaban gawar mahaifiyar tasa tare da sauran 'yan gidan sarautar Birtaniya.

Yayin da ake ajiye da gawar a Westminster Hall, akwai sojoji na musamman da za su kula da gawar har sai an tafi da ita.

A ina za a binne Sarauniyar?

Tafiya ta karshe da gawar Sarauniyar za ta yi, ita ce zuwa cocin St George da ke Fadar Windsor Castle.

Bayan an isa can da ita, za a saka ta cikin wani rami na siminti da aka gina domin 'yan gidan sarauta.

Kuma sunan wurin da za a saka ta King George VI chapel.

Mijin Sarauniyar wato Yarima Phillip wanda ya mutu a bara, da mahaifan Sarauniyar da kuma 'yar uwarta Gimbiya Margaret na cikin wadanda aka binne a wurin.

Shin za a ayyana ranar hutu a ranar binne Sarauniyar?

E. Daya daga cikin ayyukan farko da Sarki Charles III ya yi bayan ya zama sarki shi ne sanar da cewa ranar binne Sarauniyar ta kasance ranar hutu a Birtaniya.

Gwamnatin kasar ta ce "za a ba jama'a damar halartar hidimomin binne Sarauniyar domin girmama mutuwar Sarauniyar."

Ko za a rufe makarantu da shaguna a ranar?

An sanar da makarantu a Birtaniya cewa ana sa ran za su ba dalibansu hutu a ranar da za a binne Sarauniyar.

Ana kuma sa ran yawancin shaguna da kamfanonin kasar za su rufe kofofinsu a ranar.

Sai dai ba tilas ne kowa ya ki yin aiki a ranar ba.

Ko za a ayyana wasu ranakun a matsayin na hutu?

Kawo yanzu ba a tantance haka ba, amma za a dauki mataki da lokacin ya karato.

Sai dai gwamnati ta ce babu wani shiri na mayar da ranar mutuwar Sarauniya ya kasance ranar hutu a kowace shekara.

Ko za a soke wasu abubuwan da aka saba na yau da kullum?

Gwamnati ta ce babu dalilin tilastawa hukumomi su soke abubuwan da aka saba yi a kasar a wannan lokacin da ake zaman makoki.

Amma gwamnatin ta ce dukkan wadanda suka shirya wasannin motsa jiki ko na kwallon kafa za su bukaci sauya ranakun yin su idan sun ci karo da ranar da za a binne Sarauniyar.

Kuma tuni ma aka soke wasu wasannin kwallon kafa da na tseren doki da kuma na shakatawa da ake yi kamar na wasan kwaikwayo.