Iran ta bar Isra'ila da ƙasashen Yamma cikin zullumi kan ramuwa kisan Haniyeh

Rahotonni sun ce shugaban addini na Iran ya ba da umarnin kai wa Isra'ila hari kai-tsaye

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rahotonni sun ce shugaban addini na Iran ya ba da umarnin kai wa Isra'ila hari kai-tsaye
    • Marubuci, Hugo Bachega
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Beirut
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A birnin Jeddah na Saudiyya ranar Laraba, ƙungiyar ƙasashen Musulmi mai mamba 57 ta kira wani zaman gaggawa bayan Iran ta nemi hakan domin tattauna abubuwa da dama, ciki har da kisan shugaban sashen siyasa na ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran ɗain a makon da ya gabata.

Taron wata dama ce ga Iran, wadda shugaban addininta Ayatollah Khamenei ya ci alwashin "kakkausan martani" game da kisan, domin bayyana dalilanta na ramuwar.

Iran da Hamas sun zargi Isra'ila da aikata kisan na ranar 31 ga watan Yuli, wadda har yanzu ba ta ce komai ba amma kuma an yi imanin itan ce ta aikata.

Baqeri Ali Bagheri Kani, muƙaddashin ministan harkokin waje na Iran, ya ce ƙasarsa "ba ta da wani zaɓi" illa ramuwa, amma kuma za su yi hakan ne "a lokacin da ya dace da kuma yadda ya dace".

Mista Kani ya siffanta irin martanin da Iran ɗin za ta iya mayarwa a matsayin "ba wai kawai don ta kare 'yancinta ba da kuma tsaron ƙasa" akwai ma "ba da kariya ga zaman lafiyar yankin baki ɗaya".

An kashe Haniyeh ne a wani gida mai cike da tsaro da ke hannun rundunar juyin juya hali ta Iran Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), wadda ita ce mafi ƙarfin iko a ƙasar, lokacin da ya kai ziyara Tehran don shaida bikin rantsar da sabon Shugaban Ƙasa Masoud Pezeshkian.

Lamarin abin kunya ne ga hukumomin tsaron Iran.

Tun daga lokacin, duk wata alama, duk wata sanarwa da ke fitowa daga Iran na jan hankali don ganin ko akwai wani bayani kan martanin da za ta mayar, yayin da ake fargabar hakan zai jawo rikici a yankin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma Mista Kani bai ba da wata alama ba, kuma ganin yadda ƙasashen Yamma ba su da iasassun bayanan sirri kan hakan, ba a san abin da Iran ke shiryawa ba.

A watan Afrilu, harin da ake zargin Isra'ila da kaiwa a Damascus na Syriya kan wani ginin ofishin jakadancin Iran ya kashe dakarun rundunar IRGC takwas.

Bayan ɗaukar kwanaki tana nuna aniyarta, Iran ta ƙaddamar da hari da makamai fiye da 300 a kan Isra'ila, waɗanda aka tare kusan dukkansu sakamakon makaman kariyar Isra'ila da kuma ƙawancen ƙasashen da Amurka ta jagoranta a lokacin, abin da ya sa ramuwar ba ta yi wani tasiri ba.

A makon da ya gabata, jami'an Amurka sun nuna cewa a wannan karon Iran za ta iya kai hari mafi muni, musamman ƙila don ta guje wa afkuwar wancan matsalar.

Rahotonnin kafofin yaɗa labarai na baya-bayan nan sun nuna cewa salon da aka bi wajen kashe Haniyeh - babu mamaki daga cikin Iran ɗin maimakon hari ta sama daga wajen ƙasar - da kuma ganin ba a kashe ɗan Iran ko ɗaya ba, da kuma yadda ƙasashen Larabawa da na Yamma suke rarrashinta, Iran za ta iya sauya shawara.

Ministan Harkokin Waje na Jordan ya kai ziyara Iran irin wadda ba a saba gani ba a makon nan ranar Laraba, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi magana da Shugaba Pezeshkian ta waya kuma, a cewar fadar shugaban Faransa, ya neme shi da "ya yi bakin ƙokari wajen guje wa rura wutar yaƙi".

A gefe guda kuma, ana ta tsimayin hari a kan Isra'ila daga Hezbollah, ƙungiyar da Iran ke mara wa baya a Lebanon.

Ƙungiyar ta ci alwashin mayar da martani kan kisan babban kwamandanta da Isra'ila ta yi, Fuad Shukr, wanda ya faru 'yan awanni kafin kashe Haniyeh.

Fargabar faɗawa cikin yaƙi na ƙaruwa a Lebanon tun lokacin da Hizbollah ta ƙara yawan hare-hare kan Isra'ila, kwana ɗaya bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

An fi kai hare-haren ne a kan iyakar Lebanon da Isra'ila, inda Hezbollah da Isra'ila har yanzu ke nuna ba su son lamarin ya zama cikakken yaƙi.

Zuwa yanzu ƙungiyar ta fi kai wa sansanin sojan Isra'ila hare-hare, duk da cewa tana ƙarfin kai hari cikin Isra'ilar.

Shugaban Hizbollah Hassan Nasrallah, wanda ya lashi takobin martani "mai tsanani" kuma "isasshe", ya siffanta Shukr a matsayin ɗaya daga cikin "zuciyoyin gwagwarmaya masu hazaƙa", kuma ya ce sun yi magana ta waya awa ɗaya kafin mutuwarsa.

An kashe Haniyeh a wani gida mai tsattsauran tsaro da ke tsakiyar Tehran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kashe Haniyeh a wani gida mai tsattsauran tsaro da ke tsakiyar Tehran

A baya dai, Hezbollah ta rama kisan kwamandojinta ta hanyar harba makaman roka a kan Isra'ila. Ganin girman mutumin da aka kashe mata akwai yiwuwar zai jawo martani mai zafi, amma dai za ta kai shi ne cikin dokokin yaƙi kamar yadda ta bayyana.

A Lebanon, mazauna ƙasar na ganin ƙungiyar na jefa su cikin yaƙi ne yayin da har yanzu suke iya tuna yaƙin da Isra'ilar ta gwabza da Hezbollah a 2006.

Iran ba za ta so a karya lagon Hezboallah ba saboda yadda take a matsayin wani ɓangare na garkuwarta a bakin ƙofar Isra'ila.

Isra'ila na kallon shirin Iran na mallakar nukiliya a matsayin barazana, kuma Hezbollah za ta iya tare wa Iran faɗan idan aka kai wa masana'antun na Iran hari.

Hezbollah ce babba a ƙawancen da ake kira Dakarun Gwagwarmaya da Iran ke mara wa baya a faɗin yankin, da suka haɗa da Houthi na Yemen, da Hamas a Falasɗinu, da ƙananan ƙungiyoyi a Iraƙi da Syria.

Babu tabbas ko Iran da ƙawayenta za su haɗa gwiwa wajen kai harin ramuwar, duk da cewa kafofin yaɗa labarai a Amurka sun ce Hezbollah za ta iya kai nata harin ita kaɗai.

A wannan makon, Janar Michael Kurilla, shugaban bataliyar Amurka, ya kai ziyara Isra'ila domin duba shirye-shirye, kuma ana sa ran Amurka za ta sake jagorantar yunƙurin kare Isra'ila idan Iran ta kawo harin.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci alwashin "ramuwar gayya kan duk wani hari a kanmu, daga duk inda yake".

Yayin da ake cigaba da jira, kamfanoni na cigaba da sokewa ko dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa Lebanon da Isra'ila, wasu kuma na guje wa sararin samaniyar ƙasashen, su kuma ƙasashen Yamma na roƙon mutanensu su fice.

Wasu mutanen na shirin shiga yaƙi kuma yankin ka iya faɗawa cikinsa da gangan ko cikin kuskure.