Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta dauki Nkunku daga RB Leipzig kan fam miliyan 52
Chelsea ta dauki dan kwallon tawagar Faransa, Christopher Nkunku daga RB Leipzig kan fam miliyan 52.
Mai shekara 25 ya ci kwallo 16 a wasa 25 a gasar Bundesliga a kakar da ta wuce.
Nkunku, wanda ya buga wa Faransa wasa 10, shine na farko da sabon kociya, Mauricio Pochettino ya dauka, tun bayan da ya koma Chelsea a watan Mayu.
Nkunku, wanda zai koma Chelsea daga ranar 1 ga watan Yuli, ya dauki Ligue 1 uku da French Cups lokacin da ya taka leda a Paris St-Germain daga baya ya koma Leipzig a 2019.
Shine aka bayyana gwarzon Bundesliga da fitatcen dan kwallo da kungiyar 'yan wasan ta Jamus ta zaba a 2021-22, bayan da ya ci kwallo 20, sannan ya bayar da 15 aka zura a raga a lik.
Nkunku ya ci kwallo a wasan karshe a gasar German Cup a watan nan, inda Leipzig ta lashe kofin karo na biyu a jere.
RB Leipzig ta kare a mataki na uku a Bundesliga, kenan za ta wakilci Jamus a gasar zakarun Turai mai zuwa.
Nkunku ya fara buga wa Faransa tamaula a bara, amma bai buga gasar kofin duniya ba da aka yi a Qatar a 2022 ba, sakamakon raunin da ya ji.