Shekara 20 da faruwar mummunan hatsarin jirgin ruwan da mutum 1,800 suka mutu

Shekara 20 da faruwar mummunan hatsarin jirgin ruwan da mutum 1,800 suka mutu
An wallafa

A ranar 26 ga watan Satumban 2002 ne, wani katafaren jirgin ruwa mallakin ƙasar Senegal ya kife a kusa da gaɓar tekun Gambiya, inda mutum fiye da 1,800 suka mutu, yayin da 64 suka tsira.

An ayyana shi a matsayin hatsari na biyu mafi muni da ba na yaƙi ba a tarihin duniya, inda mutanen da suka mutu suka fi na jirgin Titanic yawa, amma al’amura da yawa sun dabaibaye abin da ya jawo.

A lokacin da aka shekara 20 da faruwar hatsarin, wani bincike mai taken  'The Joola: Africa’s Titanic', ya gano dalilin faruwar hatsarin.

Ya kuma bayar da labarin masifar da aka gani, ta hanyar jin ta bakin wasu daga cikin waɗanda suka tsira da iyalan wasu da suka mutu, da har yanzu suke kira da a kwaso tarkacen jirgin.