Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Kabir
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Kabir
An wallafa
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Sheikh Muhammad Kabir.
Malamin ya ce ba lokacin da ya fi jin dadi kamar lokacin da mahaifinsa ya ba shi dama ya hada karatun gida da na zamani.
Sannan abin da ya fi faranta masa rai shi ne nazarce-nazarce da rubuce-rubuce da ilimi.
Sheik Muhammad Kabir wanda ya yi digirin-digirgir, ya rubuta littattafai da dama wadanda sun kai kusan goma da ake karantar da 'yan sakandire da wasu daga cikin littattafan.