Real Madrid na shirin fuskantar Valladolid a La Liga

An wallafa

Real Madrid ta yi atisaye na uku a makon nan a kokari da take na buga wasan mako na 27 a La Liga.

Ranar Lahadi Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Real din ta yi atisayen ne a lokacin da Carlo Ancelotti ke karbar 'yan wasan da suka koma Madrid, bayan buga wa kasashen su wasannin.

Tuni kungiyar ta yi wa Ceballos da Nacho da Carvajal da kuma Modric lale a ranar Alhamis.

'Yan wasan sun motsa jiki, sannan kowa ya dauki kwallo ya yi ta wasa, daga nan aka raba kwallo a dan karamin fili.

Daga nan suka karkare da lailaya kwallo da rabawa tsakanin 'yan wasa da kuma gwada gola.

Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 68, bayan mako 26, sai Real Madrid ta biyu da maki 56, sannan Atletico ta uku da maki 51.

Wasannin mako na 27 da za a buga a La Liga a karshen mako:

Ranar Juma'a 31 ga watan Maris

  • Real Mallorca da Osasuna

Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu

  • Girona da Espanyol
  • Athletic Bilbao da Getafe
  • Cadiz da Sevilla
  • Elche da Barcelona

Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu

  • Celta Vigo da Almeria
  • Real Madrid da Real Valladolid
  • Villarreal da Real Sociedad
  • Atletico Madrid da Real Betis

Ranar Litinin 3 ga watan Afirilu

  • Valencia da Rayo Vallecano