Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu bakwai kan wasan Bayern da City a Champions League
Manchester City za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan farko zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata a Etihad.
City ce ke rike da Premier League na bara, wadda take mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Arsenal ta daya.
Bayern ita ce ta daya a teburin Bundesliga, mai rike da kofin babbar gasar tamaula ta Jamus na bara.
City ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da RB Leipzig, ita kuwa Bayern ita ce ta yi waje da Paris St Germain.
Jerin wasu batutuwa bakwai kan wasan Manchester City da Bayern Munich
1. Karawar zagayen quarter finals a Champions League:
Kawo yanzu Bayern Munich ta ci wasa takwas a gasar zakarun Turai ta bana, karo na biyu tana wannan bajintar bayan 2019/20.
Ba wata kungiya fiye da ita da ta ci wasa takwas tun bayan da aka soke karawar rukuni a zagaye na biyu, wanda ya koma wasa gida da waje.
Wannan shine karo na 21 da Bayern ta kai quarter finals a Champions League, wadda ta dara Real Madrid mai 19.
Manchester City ce kadai cikin masu kai wa zagayen daf da na kusa da na karshe a kaka shida a jere a baya.
2. Karawa tsakanin kungiyoyin biyu a Champions League:
Wasa na karshe tsakanin City da Bayern shine na 2014, wanda kungiyar Ingila ta yi nasara a gida da cin 3-2.
Kowacce ta ci uku-uku, wannan shine wasan farko da za su kece raini a zagayen quarter finals, a cikin rukuni suka kara a baya a fafatawa shida.
Wasa shida tsakanin Man City da Bayern Munich
Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2014
- Man City 3 - 2 B Munich
Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2014
- B Munich 1 - 0 Man City
Champions League Tu 10Dec 2013
- B Munich 2 - 3 Man City
Champions League We 02Oct 2013
- Man City 1 - 3 B Munich
Champions League We 07Dec 2011
- Man City 2 - 0 B Munich
Champions League Tu 27Sep 2011
- B Munich 2 - 0 Man City
Bayern ta kai zagayen gaba a wasa biyar daga shida da ta fuskanci kungiyoyin Ingila a ziri kwalle, in banda kakar 2018/19 a zagaye na biyu da Liverpool.
Bayern ta ci wasa hudu a jere a kan kungiyoyin Premier League, kuma ba a doke ta ba a karawa hudu da ta kai ziyara Ingila, wadda ta ci uku da canjaras daya.
Sai dai City ta ci wasa 10 a jere a gida a kan kungiyoyin Jamus a Champions League da cin kwallo 39 -10.
3. Ba a ci kungiyoyin biyu kwallaye da yawa ba a Champions League:
Kwallo biyu ne ya shiga ragar Bayern, yayin da uku aka zura wa City a raga a bana a Champions League.
Wasa bakwai Bayern ta yi kwallo bai shiga ragarta ba, a karawa da Viktoria Plzen ne Bayern ta yi nasara da cin 4-2, sune biyun da aka zura mata a raga.
4. Watakila Muller ya kafa tarihi a Champions League:
A wasan da Bayern ta doke Paris St Germain a karawa ta biyu zagayen 'yan 16, karo na 99 da aka yi nasara da Thomas Muller a Bayern Munich daga wasa 140.
Zai zama na uku da aka ci wasa 100 da shi a Champions League, bayan Cristiano Ronaldo mai 115 a Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus.
Sai kuma na biyu Iker Casillas mai 101 a Real Madrid da Porto.
Sai dai Muller zai kafa nasa tarihin a kungiya daya Bayern Munich.
5. Wasan farko da Tuchel zai ja ragamar Bayern a Champions League:
Thomas Tuchel, mai shekara 49 ya lashe Champions League a Chelsea, kenan ya san dadin kofin da ya dauka bayan cin City 1-0 a wasan karshe.
Wasa na uku baya da ya fuskanci Pep Guardiola kenan.
Tuchel a Chelsea ya ci City 1-0 a FA Cup daf da karshe a Afirilun 2021, Tuchel ya yi rashin nasara a Borussia Dortmund a 2016 a DFB Cup karawar karshe a bugun fenariti a hannun Guradiola a Bayern, bayan da suka tashi 0-0 a minti 120.
6. Na daya a cin kwallaye da na farko a yawan bayarwa a zura a raga:
Erling Haaland ya ci wa Man City kwallo 10 a Champions League a kakar nan.
Ba bako bane wajen cin kwallaye a gasar, wanda ya zura 33 a wasan farko 25 da ya yi a gasar.
Wato yana da tazarar 13 ga duk dan wasan da ya ci kwallo a karawa 25 a farkon fara Champions League.
Bayern tana da 'yan wasa biyu da ke kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga a bana da ya hada da Joao Cancelo mai wasan aro daga City, wanda ya bayar da biyar.
Na biyu kuwa shine Leon Goretzka wanda ya bayar da hudu aka zura a raga.
7. Karawa ta zakarun lik din kasashensu:
Bayern da Man City daya ne daga wasa hudu a zagayen quarter finals tsakanin masu rike da kofin lik din kasarsu.
Bayern Munich tana da Champions League shida, ita kuwa City ba ta taba lashe kofin ba, duk da Guardiola yana da biyu a Barcelona.