Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Howe ya ce Ingila ba ta tuntuɓe shi kan aikin kociyanta ba
Kocin Newcastle United, Eddie Howe ya ce hukumar kwallon kafar Ingila ba ta tuntuɓe shi ba game da aikin kocin Ingila.
Howe na daga cikin waɗanda ake alakantawa da aiki, bayan Gareth Southgate ya ajiye aiki a ranar 16 ga watan Yuli, bayan Euro 2024.
"Babu wata tuntuɓar a tsakaninmu," in ji Howe lokacin da aka tambaye shi game da aikin kocin Ingila lokacin da Newcastle ta sauka a Japan.
Shugaban gudanarwar Newcastle, Darren Eales ya ce kungiyar ta kuduri aniyar ci gaba da aiki da Howe, kuma za ta yi watsi da duk wata hanya daga hukumar kwallon kafa ta Ingila wajen son ɗaukar kocin.
Ƙungiyar St James Park ta kare a matsayi na bakwai a gasar Premier a shekarar 2023-24, kuma za ta fara wasan farko a bana da Southampton ranar 17 ga Agusta.
Ranar 7 ga watan Satumba, Ingila za ta buga Nations League, inda za ta kara da Jamhuriyar Ireland a Dublin.
Karon farko da za ta kara tun bayan da Southgate ya ajiye aikin, bayan da kasar ta kasa lashe Euro karo biyu a jere da ta kai wasan karshe.
Haka kuma bayan Howe da ake alakantawa da aikin kociyan Ingila, sauran sun hada da mai horar da ƴan kasa da shekara 21 na kasar, Lee Carsley da Graham Potter da Jurgen Klopp da kuma Thomas Tuchel.