Hawan Daushe a masarautar Kano

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Hawan Daushe a masarautar Kano
An wallafa

Hawan Daushe a masarutar Kano hawa ne da sarki ke yi da yammacin washe garin sallah, wato kwana ɗaya bayan sallah.

A al'adar masarautar Kano, Sarki kan yi hawan ne daga fadarsa zuwa Gwangwazo domin gayar da mahaifiyarsa, wato gidan mai babban ɗaki.

Hawa ne da duka hakiman masarautar kan fito tare da tawagoginsu, domin yin gaisuwa ga sarki.

Haka kuma hawa ne da hakimai kan kece raini ta fuskar ado ko kwalliya, domin nuna isa da ƙasaita, irin ta sarauta.