Jamus ta lallasa Bosnia da ci bakwai da nema

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan Arsenal Kai Havertz na daga cikin 'yan kwallon Jamus da suka lallasa Bosnia-Herzegovina da ci bakwai da nema.

A yanzu haka Jamus ce ke kan gaba a saman teburin rukunin da ta ke.

Kuma Jamus ta kafa tarihi a matsayin kasa ta farko da ta zura kwallo bakwai a wasa daya a gasar Nations League.

Jamal Musiala ne ya fara cin kwallo a minti na biyu da soma wasan.

T. Kleindienst kuma ya ci kwallo biyu sai K. Havertz da ya ci kwallo daya.

Wadansu 'yan wasan da suka zura kwallo a wasan su ne; Wirtz da kuma Sané duk sun ci kwallo a wasan.

A yanzu Jamus ta tsallake zuwa zagayen gab da na kusa da karshe wanda za a buga a cikin watan Maris.