Ƙafar United ɗaya ta kai wasan ƙarshe a gasar Europa League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙafar Manchester United guda ta kai wasan ƙarashe na gasar Zakarun Turai ta Europa League bayan da ta doke Athletic Bilbao da ci 3-0 a Sifaniya.

Da fari wasan ya nuna kamar ba zai yi wa United kyau ba, to amma bayan minta 30 sai wasan ya sauya bayan da Harry Maguire ya yi wata bajinta tare da buga ƙwallo zuwa da'irar bilbao, lamarin da ya bai wa Casemiro damar zura ƙwallon farko a wasan.

Minti uku bayan nan ne United ta ƙara samun wata damar bayan da ɗan wasan bayan Bilbao, Dani Vivian ya yi wa Rasmus Hojlund ƙeta a yadi na 18, inda bayan duba na'urar taimaka wa alƙalin wasa ta VAR, aka bai wa Vivian jan kati tare da bai wa United bugun fenareti.

Bayan da Bruno ya buga fenaretin ya kuma ci, ya ƙara ta uku kafin tafiya hutun rabin lokaci bayan da ɗan wasan Bilbao ya yi kuskure.

A mako mai zuwa ne United - wadda kofin Europa ne kawai fatanta a wannan kaka - za ta karɓi baƙunci Bilbao a filin wasa na Old Trafford.

A ɗaya wasan na Europa kuwa, Tottenham ce ta samu nasara kan Bodø/Glimt da ci 3-1 a Ingila.

Masu nazarin ƙwallon ƙafa na hasashen buga wasan ƙarshe tsakanin ƙungiyoyin Ingila, United ta Tottenham a gasar ta Europa, wani abu da aka jima ba a gani ba.

Can ma a ƙaramar gasar ta Conference League, Chelsea ta samu nasarar doke Djurgården da ci 4-1, wadda ita ma ake hasashen za ta kai wasan ƙarshe na gasar.

A mako mai zuwa ne Arsenal za ta je gidan PSG a babbar gasar Zakatun Turai ta Champions League, da nufin ɗaukar fansa kan ci 1-0 da PSG ta yi mata a Emirates.