Hikayata 2024: Labarai 15 da suka yi fice a bana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A matakin ƙarshe na tantance labaran da suka yi fice a gasar rubutun gajeru ƙagaggun labarai ta mata zalla wato Hikayata ta bana, alƙalan gasar sun zaɓi labarai guda 15 da suka ce su ne suka yi fice a gasar ta bana.

Harwayau alƙalan sun kuma zaɓi labarai guda uku da suka zama zakaru waɗanda nan gaba kaɗan za mu wallafa su.

Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30.

Daga cikin 30 din ne kuma alƙalan na ƙarshe suka zaɓi guda 15, inda uku daga ciki suka zaman zakaru sannan 12 suka cancanci yabo.

  • Buɗaɗɗiyar wasiƙa
  • Zamani Riga
  • Mugun Nama
  • Halitta Biyu
  • Unguwar Zoma
  • Mafitarmu
  • Wanda Ya Ƙi Ji
  • Magaribar Jaki
  • Naɗin Jaki
  • Biyu Babu
  • Amon 'Yanci
  • Kura A rumbu
  • Tsalle Ɗaya
  • Tsayuwar wata
  • Yi wa Kai

A ranar 27 ga watan nan na Nuwamba ne dai za a gudanar da bikin karrama gwarazan a Abuja, babban birnin Najeriya.

Waɗanda suka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan ɗaya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu ɗari biyar) ga wadda ta zo ta uku.

BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.