Cucurella ya kai Chelsea mataki na huɗu a teburin Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta koma mataki na huɗu a teburin Premier League bayan da ta yi nasara a kan Leicester City da ci 1-0 ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Marc Cucurella ne ya ci ƙwallon kuma na biyar a kakar nan na biyu a jere, bayan da ya jefa a ragar Southampton.

Chelsea ta samu bugun fenariti, bayan da Victor Kristiansen ya yi wa Jadon Sancho keta a karawar ta mako na 28.

Cole Palmer ne ya buga fenaritin, amma bai ci ƙwallon ba, hakan ya sa ya zama karon farko da bai ci bugun fenariti ba, bayan 12 da ya zura a raga.

Kawo yanzu Palmer ya yi karawa tara bai ci ƙwallo ba tun bayan ɗayan da ya zura a ragar Bournemouth da suka tashi 2-2 ranar 14 ga watan Janairu.

Leicester ta ci gaba da zama ta biyun karshen teburi wato ta 18 da rarar ƙwallaye tsakani da Ipswich da tazarar maki shida tsakani da Wolves ta 17 teburi.

Ranar Alhamis Chelsea za ta karɓi bakuncin Copenhagen a Europa Conference League daga nan ta je Arsenal a Premier League ranar 16 ga watan Maris.