Man United ta sha da ƙyar a gidan Everton a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Everton da Manchester United sun tashi 2-2 a Premier League ranar Asabar a Goodison Park.
Everton ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Beto a minti na 19 da fara wasan, kuma na shida kenan da ya zura a raga a gasar bana.
Daga baya ne Abdoulaye Doucoure ya kara na biyu, kuma haka suka je hutu, Everton na cin United 2-0 a wasan mako na 26.
Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne United ta zare ɗaya ta hannun ƙyaftin, Bruno Fernandes, sannan Manuel Ugarte ya farke na biyu.
Tun kafin karawar ta ranar Asabar, United ta doke Everton 4-0 a Old Trafford a wasan farko a bana a Premier League ranar Lahadi 1 ga watan Disamba.
Kuma karon farko da Everton ta buga wasa da United ta na saman ƙungiyar Old Trafford a teburi tun bayan 20 ga watan Afirilun 2014.
Da wannan sakamakon Everton tana mataki na 14 a kan teburi da maki 31, bayan cin wasa bakwai da canjaras 10 da rashin nasara tara.
Ita kuwa United ta ci gaba da zama a mataki na 15 da maki 30, wadda ta yi nasara takwas da canajaras shida aka doke ta wasa 12.
United za ta karɓi bakuncin Ipswich Town ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu a gasar Premier, daga nan ta buga FA Cup da Fulham ranar Lahadi 2 ga watan Maris.












