Arsenal na shawara kan Fofana, kuma ba ta cire tsammani ba kan Alvarez

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na shawara kan ɗanwasan gaba na Lyon da Belgium mai shekara 21 Malick Fofana kafin rufe kasuwar cinikin yanwasa a ranar Talata. (RMC Sport - in French)

Haka kuma Gunners har yanzu ba ta haƙura ba da buƙatar ɗauko ɗanwasan Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez kuma tana son ɗauko ɗanwasan cikin sauƙi. (Teamtalk)

Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 na Nottingham Forest kan ɗanwasan tsakiya mai shekara 20 Trey Nyoni, 19. (Athletic - subscription required)

Borussia Dortmund na diba yiyuwar ba Jadon Sancho dama tafiya amma ɗanwasan na Ingila dole sai ya amince da yarjejeniyar da za ta tabbatar da ƙwazon sa. (Bild - in German)

Newcastle ta amince da yarjejeniya da Lille domin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Belgium Matias Fernandez-Pardo kan yarjejeniyar shekara biyar. (Athletic - subscription required)

Ajax ta tuntuɓi Sundaland kan ɗanwasan gaba na Ivory Coast Simon Adingra. (Telegraph - subscription required)

Fulham ta soma tattaunawa da Eintracht Frankfurt kan ɗanwasan ƙasar Sweden Hugo Larsson. (Fabrizio Romano)

Newcastle da Juventus sun cimma yarjejeniya kan bayar da aron ɗanwasan gaba na Jamus Nick Woltemade. (Florian Plettenberg)

Ɗanwasan gaba na Arsenal da Ingila Ethan Nwaneri, mai shekara 19, na cikin ƴanwasan da Borussia Dortmund ke hari. (Sky Germany)