Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Alvarez zai koma buga wa Atletico Madrid wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 31 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan Satumba 2026.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Mohammed, Haruna Kakangi, Buhari Fagge

  1. Me kuke son sani kan wasan Premier League mako na uku, Premier League

    Ranar Asabar 5 ga watan Satumba

    Brentford (5) v Sunderland (11)

    Mathias Jensen ba zai samu damar buga wa Brentford wasan ba. Har yanzu Josh Dasilva na hutu bayan raunin da ya yake jinya, amma babu wani sabon ɗan wasa da yake jinya.

    Habib Diarra ba zai buga wa Sunderland wasan ba, saboda raunin da yake jinya, inda zai shafe mako shida zuwa takwas. Kevin Danso da Malick Fofana da kuma Juan Riquelme Angulo sun koma ƙungiyar a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar cinikayya ƴan ƙwallo.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Brentford 3 Sunderland 0, Sunderland 2 Brentford 1

    Alƙalin wasa: Thomas Bramall (Sheffield)

    Brighton (9) v Leeds (8)

    Dan wasa Chema Andres zai iya buga karawar a wasansa na farko a Brighton, amma sabon ɗan wasan da aka saya a ranar rufe kasuwa, Femi Azeez, ba zai buga ba, saboda wani rauni da yake jinya. Mats Wieffer ma ba zai buga karawar ba, wanda ba zai samu yin karawa hudu ba.

    Yasin Ayari da Georginio Rutter na iya buga wasan, amma Jack Hinshelwood da Yankuba Minteh da Kaoru Mitoma da Stefanos Tzimas duk suna jinya.

    Leeds za ta ci gaba da buga tamaula ba tare da Joe Rodon ba har tsawon mako takwas zuwa 10, saboda raunin da yake jinya. Haka kuma Gabriel Gudmundsson na iya fara buga wasa a kakar bana, bayan zaman benci a wasan Brentford, yayin da sababbin 'yan wasan da aka aro a ranar ƙarshe ta kasuwa, Melvin Bard da Jean-Matteo Bahoya, su ma na iya kasancewa a cikin ƙungiyar.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Leeds 1 Brighton 0, Brighton 3 Leeds 0

    Alƙalin wasa: Stuart Attwell (Warwickshire)

    Fulham (16) v Crystal Palace (18)

    Alvaro Arbeloa ya ba da shawarar cewa tana yiwuwa ya saka sababbin 'yan wasan da Fulham ta saya a ranar karshe ta kasuwa, wato Manuel Angel da Hugo Larsson da David Affengruber a cikin 'yan wasan ƙungiyar, sai dai ya ce suna iya kasancewa a kan benchi.

    Ƴan wasan Palace guda uku, Ismaila Sarr da Jean-Philippe Mateta da Chadi Riad har yanzu ba za su buga wasan ba, saboda jinya. Sababbin 'yan wasan da aka saya a ranar rufe kasuwa, Ben Chilwell da Dario Osorio da Quinten Timber na iya kasancewa a cikin jerin ƴan wasan, yayin da Palace ke neman samun maki bayan shan kashi da fara kakar bana.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Crystal Palace 1 Fulham 1, Fulham 1 Crystal Palace 2

    Alƙalin wasa: Sam Barrott (West Yorkshire)

    Hull (3) v Aston Villa (19)

    Ɗan wasan Hull, Joe Gelhardt na iya komawa cikin ƴanwasa, yayin da ake sa ran Nobel Mendy zai iya buga wasan, bayan da ya murmure. Sai dai Jack Butland da Charlie Hughes da Eliot Matazo da Hidemasa Morita da Oscar Zambrano da Darko Gyabi ba za su buga fafatawar ba.

    Aston Villa har yanzu ta rasa Johan Manzambi da Joao Gomes. Sababbin 'yan wasan da ta saya, Taylor Harwood-Bellis da Ibrahim Mbaye da Leon Goretzka na iya kasancewa a cikin ƴanwasan.

    Alƙalin wasa: Michael Oliver (Northumberland)

    Manchester City (1) v Coventry (17)

    Enzo Fernandez da Iliman Ndiaye duka na iya yin wasansu na farko a Manchester City biyo bayan komawarsu ƙungiyar a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar cinikayya. Matheus Nunes ya koma taka leda bayan da ya warke daga jinya, amma Jeremy Doku har yanzu yana jinya.

    Frank Onyeka ya warke zai buga wa Coventry wasan, haka shima Bobby Thomas ya ji sauki, yayin da za a ci gaba da sa ido kan lafiyar Sidiki Cherif.

    Alƙalin wasa: Paul Tierney (Lancashire)

    Newcastle (6) v Bournemouth (14)

    Newcastle za ta kasance ba tare da Dan Burn da Joelinton da Will Osula ba, yayin da Tino Livramento ke iya dawowa cikin ƴanwasan. Sabon ɗan wasan da aka saya a ranar ƙarshe ta kasuwa, Matias Fernandez-Pardo, yana da damar yin wasansa na farko.

    Bournemouth ba ta da wata damuwa ta raunin ƴan wasa. Julian Araujo da Junior Kroupi da Amine Adli da Veljko Milosavljevic duk za su ci gaba da jinya.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Newcastle 1 Bournemouth 2, Bournemouth 0 Newcastle 0

    Alƙalin wasa: Robert Jones (Merseyside)

    Nottingham Forest (15) v Tottenham (20)

    Daniel Munoz a shirye yake ya yi wasansa na farko a Forest duk da cewa ɗan ƙasar Colombia yana ci gaba da atisaye sanye da takunkumin fuska biyo bayan tiyatar da aka yi masa a hanci. Ana shakku kan Ibrahim Sangare saboda raunin ƙafa da ya hana shi buga wasan mako da ya gabata da suka tashi 2-2 da Liverpool.

    Sabon ɗan wasan da aka saya, Mykhailo Mudryk, yana da damar yin wasansa na farko a Spurs a filin wasa na City Ground. Roberto De Zerbi ya tabbatar da cewa za a yi gwajin ƙarshe kan lafiyar James Maddison, amma Dejan Kulusevski da Xavi Simons da Wilson Odobert suna jinya.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Tottenham 0 Nottingham Forest 3, Nottingham Forest 3 Tottenham 0

    Alƙalin wasa: Craig Pawson (South Yorkshire)

    Ranar Lahadi 6 ga watan Satumba

    Arsenal (2) v Chelsea (4)

    Jurrien Timber na iya dawowa ci gaba da buga wa Arsenal wasanni. Bruno Guimaraes da Cristhian Mosquera za a ci gaba da auna koshin lafiyarsu.

    Chelsea za ta yanke shawara kan ɗan wasa, Moises Caicedo, wanda ya fita a karshen wasan da suka yi nasara a kan Brighton. Jordan Henderson yana daf da komawa atisaye gadan-gadan biyo bayan raunin tsintsiyar hannu da ya samu a gasar Kofin Duniya, yayin da ɗan wasa, Emmanuel Emegha yake ci gaba damurmurewa.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Arsenal 2 Chelsea 1, Chelsea 1 Arsenal 1

    Alƙalin wasa: Christopher Kavanagh (England)

    Everton (7) v Manchester Utd (10)

    David Moyes na iya saka sababbin 'yan wasan da ya saya a bazarar nan, Jack Grealish da Ainsley Maitland-Niles, yayin da fitar Iliman Ndiaye ta buɗe wa Brennan Johnson damar buga gurbin ɓangaren dama. Sai dai kuma, wani sabon ɗan wasan da aka saya a bazara, Christian Norgaard, har yanzu yana jiyyar raunin da ba a bayyana ba.

    Carlos Baleba da Amad Diallo har yanzu ba za su buga wa United wasan ba. Mason Mount yana ta kokarin dawowa cikin ƴan wasan United, yayin da Matthijs de Ligt ke ci gaba da jiyyar raunin bayansa na dogon lokaci. Manuel Ugarte shi ma ba zai buga karawar ba.

    Sakamakon kakar da ta gabata: Everton 0 Manchester Utd 1, Manchester Utd 0 Everton 1

    Alƙalin wasa: John Brooks (Leicestershire)

  2. Alonso na son Chelsea ta kara kokari bayan tafiyar Fernandez zuwa Man City, Enzo Fernandez

    Kocin Chelsea Xabi Alonso na fatan ƙungiyar za ta kara kokari, bayan sayar da Enzo Fernandez zuwa Manchester City wanda aka tabbatar da hakan a daren ranar rufe kasuwar cinikayyar ƴanwasa.

    Ɗan wasan tawagar Argentina ya bar Stamford Bridge ya koma City kan fam miliyan 125, wanda ya yi daidai da mafi girman kudin da aka kashe kan sayen ɗan wasa a Birtaniya, kafin kasuwar ta rufe a daren Talata.

    Chelsea tun farko ta sanya ranar 14 ga watan Agusta a matsayin wa’adin da ta gindaya ga duk mai son sayen Fernandez. Amma bayan ranar ta wuce, City ta sake dawowa da wani tayin wanda ya haifar da tattaunawa da aka daɗe ana cinikin kafin daga bisani a cimma yarjejeniya kusa da karfe 11 na dare, lokacin rufe kasuwar.

    Blues din ta so sayen Lamine Camara daga Monaco, amma yarjejeniyar ta rushe bayan kungiyar Ligue 1 ta janye daga cinikin saboda ba ta sanya hannu kan takardar yarjejeniya ba, kafin rufe kasuwar ta bazara.

    Sai dai Alonso ya ce ya kamata a dauki duk abin da ya faru a matsayin abin da ya wuce, yayin da yake kokarin mayar da hankali kan yadda za su taka rawar gani a ranar Lahadi, inda za su kai ziyara gidan Arsenal mai riƙe da kofin Premier League.

  3. Ba nine na cire Richarlison daga cikin ƴanwasan Tottenham ba, Richarlison

    Kocin Tottenham Hotspur, Roberto de Zerbi ya ce ba shi ne ya yanke shawarar cire Richarlison daga cikin jerin ƴanwasan da aka mika wa Premier League ba.

    Yayin da aka saka sunan masu jinya Xavi Simons da Wilson Odobert daga 25 da Spurs ta mika wa Premier League ranar Alhamis, rashin saka ɗan wasan tawagar Brazil ya ja hankali kan makomar ɗan ƙwallon.

    A ranar Asabar, De Zerbi ya ce dan wasan mai shekara 29 ya nemi barin Tottenham kuma yana dab da komawa tsohuwar ƙungiyarsa Everton kafin wa’adin rufe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo ta cika ranar Talata, amma yarjejeniyar ta rushe.

    An alakanta Trabzonspor da zawarcin Richarlison, kuma wa’adin kasuwar cinikayya ga Turkiyya zai rufe da karfe 22:00 BST ranar Juma’a.

    Ƙungiyoyin Saudiyya na iya daukar ƴanwasa har zuwa ranar Lahadi, amma idan tsohon dan wasan Everton din ya ci gaba da zama a Spurs, ba zai cancanci taka leda a Premier League ba.

    Richarlison shi ne ya fi kowa zura kwallaye a Tottenham a gasar lig din kakar da ta gabata, inda ya zura 11 a raga a wasa 32 da ya buga, kuma ya kasance daya daga cikin manyan ƴan wasan da suka taimaka wa kungiyar wajen kauce wa daga faduwa a gasar, lamarin da aka tabbatar a ranar karshe ta kakar wasan Premier League.

  4. Ƴanwasan Real Madrid da za su je gidan Real Betis, Real Betis vs Real Madrid

    Real Madrid ta bayyana ƴanwasan da za su fuskanci Real Betis a wasan mako na huɗu a La Liga ranar Juma'a.

    Ƴanwasan Real Madrid:Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Javi Navarro.Masu tsaron baya: Huijsen, Trent, Konaté, Cucurella, Á. Carreras, Rüdiger, Dumfries da Mario Rivas.Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Arda Güler, Bernardo, Cestero da Sergio Martínez.Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, C. Espí, Brahim da Yan Diomande.

  5. Real Madrid za ta je gidan Real Betis ranar Juma'a a La Liga, Real Betis vs Real Madrid

    Real Madrid za ta buga wasan mako na huɗu a La Liga da zuwa gidan Real Betis da za su fafata a Estadio La Cartuja da fatan cin wasa na huɗu a jere da fara kakar bana.

    Shi ne wasan farko da Real Madrid za ta kara a watan Satumba. Za ta buga biyu nan gaba daga makon gobe a Santiago Bernabeu, inda za ta kece raini da Inter Milan a Champions League da kuma fuskantar Rayo a La Liga, sauran biyun sun hada da kece raini da Elche da kuma Atlético.

    Tuni Real Madrid ta bayyana ƴan wasa 23 da za su buga mata fafatawar daga ciki har da Mbappé, wanda ke ganiyar cin ƙwallaye da Bellingham.

    BetisƘungiyar da Manuel Pellegrini ke jan ragama tana kaka ta bakwai a jere a La Liga, wadda ta fara kakar bana da kafar bana tana mataki na bakwai a kan teburi, bayn cin wasa biyu da rashin nasara ɗaya, kuma karawa daga cikin biyu ƙwallo bai shiga ragarta ba, wasan da ta yi rashin nasara shi ne 1-0 a hannun Real Sociedad.

  6. Alvarez zai koma buga wa Atletico Madrid wasanni, Julian Alvarez

    Julian Alvarez zai koma cikin ƴan wasan Atletico Madrid, domin fuskantar Athletic Club a gasar La Liga, bayan da yunkurinsa na barin ƙungiyar bai yi nasara ba ya zama “darasin”, a cewar koci, Diego Simeone.

    Ɗan wasan mai shekara 26 bai yi atisayen kwana biyu ba a makon da ya gabata, yana mai cewa rashin lafiya ne ya hana shi halarta, bayan da aka sanar da shi a sirrance cewa Atletico ba za ta sayar da shi ga Barcelona ba.

    Yiwuwar komawa Arsenal ta zama hanya daya tilo da dan wasan gaban Argentina zai iya barin ƙungiyar, amma hakan bai yiwuba, kuma an mayar da shi cikin atisayen kungiyar bayan da bai buga wasan La Liga da ƙungiyar ta kara da Sevilla.

    Atletico ta fitar da sanarwa guda biyu cikin awa 24 tana sake jaddada matsayinta cewa ba za ta amince da bukatar Alvarez ta komawa abokiyar hamayyarta Barcelona ba.

    Sai dai ƙungiyar Simeone ta kasance a shirye ta sayar da Alvarez ga Arsenal kuma ta gudanar da tattaunawa kai tsaye da zakarun Premier League.

    A makon da ya gabata, Simeone ya ce zai "yi duk abin da zai iya" domin tabbatar da cewa Alvarez ya koma taka leda a ɗaya daga fitatttun ƴan wasan ƙungiyar.

    Alvarez ya zura kwallaye 49 a wasanni 107 da ya buga wa Atletico tun bayan komawarsa daga Manchester City kan fam miliyan 81 a shekarar 2024, amma har yanzu bai lashe wani kofi ba a Madrid.

    Atletico za ta je Bilbao domin fuskantar Athletic Club ranar Asabar domin buga wasannin La Liga.

  7. Llorente ya yi ritaya daga buga wa Spaniya wasanni, Spaniya

    Marcos Llorente, wanda ya lashe Kofin Duniya, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasar Sipaniya ƙwallon ƙafa a ranar Alhamis, bayan wasa 27 da ya buga wa tawagar.

    Mai tsaron baya na Atletico Madrid mai shekaru 31 ya fara bugawa babbar tawagar Spaniya wasa a shekarar 2020, kuma yana cikin ƴanwasan da suka doke Argentina da ci 1-0 suka lashe Kofin Duniya a watan Yuli da aaka yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico, kodayake ya zauna a benci a wasan ƙarshen.

    Tsohon ɗan wasan Real Madrid ya gode wa abokan wasansa tare da yin waiwaye kan nasarar da Spaniya ta samu a gasar cin Kofin Duniya.

  8. Ƴanƙwallo 20 mafi tsada da aka saya a duniya a lokacin bazara

    Ƙungiyoyin Premier League sun kafa sabon tarihin kashe kuɗi masu yawa a lokacin cinikayyar ƴanwasa a kakar wasa ta bana, inda aka kashe har fam biliyan 3.5 - sai dai mafi girman cinikin ya shafi duk wanda aka yi a fadin duniya.

    Tarihin sayayyar ƴanwasan mafi tsada da fitattun ƴanƙwallon da suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da kuma cinikin da ba a zata ba sun kasance cikin ƴanwasa 20 mafi tsada a wannan bazarar, bisa ga kuɗin da aka sanar a hukumance da BBC ta tattara rahoto.

  9. An cire Richarlison daga ƴan wasan da za su buga Premier League a karshen mako, Tottenham

    An cire Richarlison daga jerin ƴan wasan Tottenham da za su buga wasannin Premier League a karshen mako.

    Kocin Tottenham, Roberto de Zerbi, ya ce a makon da ya gabata cewa ɗan wasan tawagar Brazil ya nemi izinin ya bar ƙungiyar, kuma ya yi kamar yana dab da komawa tsohuwar ƙungiyarsa Everton kafin wa’adin kasuwar cinikin ƴan wasa ya ƙare ranar Talata daga nan yarjejeniyar ta rushe.

    Yanzu an cire ɗan wasan mai shekara 29 daga jerin waɗanda za su buga wa ƙungiyar gasar cin kofin Premier League.

    An fahimci cewa Richarlison ba ya cikin shirye-shiryen Tottenham a kakar nan, kuma an bayyana masa hakan kafin ranar Talata.

    Duk da haka, har yanzu ana sa ran zai bar ƙungiyar a cikin kwanaki masu zuwa, kasancewar kasuwar cinikin ƴan wasa a Turkiyya da Saudiyya suna nan a buɗe.

    Richarlison ya koma Tottenham daga Everton a bazarar shekarar 2022, bayan da ya koma Everton daga Watford a shekarar 2018.

  10. Martinelli ya koma Saudiyya kan fam miliyan 60, Arsenal

    Ɗan wasan Arsenal, Gabriel Martinelli ya koma ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya kan fam miliyan 60.

    Yarjejeniyar ta kuma kunshi wani kaso da zai shafi tsarabe-tsarabe ta kawo karshen zaman ɗan wasan tawagar Brazil na shekara bakwai a ƙungiyar Arewacin Landan.

    Martinelli, mai shekara 25, ya sanya hannu kan yarjejeniya ta dogon lokaci da Al-Hilal, wadda a halin yanzu take saman teburi a babbar gasar tamaula ta Saudiyya tare da Al-Nassr ta Cristiano Ronaldo.

    Ya koma Arsenal daga ƙungiyar Ituano ta Brazil a shekarar 2019, kuma saura wata 12 kwantiraginsa ya kare a filin Emirates, kuma koci Mikel Arteta ne ya sanar da shi cewa ba ya cikin tsare-tsarensa na wannan kakar wasan ta bana, dalilin da ya sa ya je ya gwada sa'a.

  11. Uefa na binciken ƴanwasan Fenerbahce, Guendouzi da Greenwood, Uefa

    UEFA ta buɗe matakan ladabtarwa kan ƴan wasan Fenerbahce Matteo Guendouzi da Mason Greenwood bayan abinda ya faru a wasa na biyu a zagayen neman gurbi a Gasar Zakarun Turai da suka buga a filin Olympique Lyonnais, kamar yadda ƙungiyar ta Turkiyya ta bayyana ranar Alhamis.

    Ana zargin ɗan wasan Faransa Guendouzi da na Ingila Greenwood da yin alamun da suka tayar da hankali ga magoya bayan Lyon, lamarin da ya haifar da cacar baki da faɗa yayin da Guendouzi ke barin fili a karawar da Fenerbahce ta samu nasara da ci 2-1 a watan da ya gabata.

    Fenerbahce ta kai matakin rukuni a Gasar Zakarun Turai bayan da ta yi nasara da jimillar ƙwallaye 3-2 gida da waje.

  12. Sarr ya harzuka da batun komawarsa Liverpool ya bi ruwa, Samaila Sarr

    Kocin Crystal Palace, Pierre Sage ya ce Ismaila Sarr zai buƙaci lokaci domin hankalinsa ya kwanta, bayan da ya harzuka, sakamakon batun komawarsa Liverpool ya rushe.

    Ɗan wasan tawagar Senegal, wanda shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Palace a kakar da ta gabata, yana gab da kammala komawa Anfield a kwanakin ƙarshe na rufe kasuwar cinikin ƴanwasa, amma daga ƙarshe ya ci gaba da zama a Selhurst Park, saboda ana kasa cimma matsaya.

    “Tabbas yana buƙatar ya natsu ya karɓi abin da ya faru da shi da ƙyaƙƙyawar niya, domin mafarki ne ga ƴan wasa da dama da suke da shi na buga wa irin wannan ƙungiya (Liverpool) wasanni,” in ji Sage gabanin shirye-shiryen Palace zuwa filin Fulham a wannan ƙarshen mako don buga gasar Premier League.

    Palace za ta je Fulham ranar Asabar yayin da dukkan ƙungiyoyin biyu har yanzu suke neman makinsu na farko a gasar Premier League bayan wasanni biyu da suka buga da fara kakar bana.

  13. An kashe sama da fam biliyan 7 a kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo, Kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo

    Kasuwar cinikayyar ƴan wasa ta duniya ta kafa sabon tarihi, inda aka samu ƙarin kuɗin da aka kashe da kuma yawan sauye-sauyen ƴan wasa fiye da na bara.

    Kuɗin musayar sun haura dala biliyan 9.8 na Amurka (fan biliyan 7.24), wanda ya nuna ƙarin fiye da kashi 1.5 idan aka kwatanta da wata 12 da suka gabata, yayin da yawan musayar ƴan wasa ya ƙaru da kashi shida zuwa 12,575, lamarin da aka kafa sabon tarihi a kasuwar cinikin ƴan wasa ta bazara.

    Bisa ga alkaluman da FIFA ta fitar a cikin rahoton International Transfer Snapshot, ƙungiyoyin Ingila ne suka jagoranci kashe kuɗi mafi yawa a duniya, inda suka zuba sama da dala biliyan 3 na Amurka (fan biliyan 2.2) a kuɗin cinikayyar, gasar Italiya kuwa (fan miliyan 810), Spain (fan miliyan 695), Jamus (fan miliyan 668) da Faransa (fan miliyan 474).

    Ƙungiyoyin Ingila kuma su ne suka kammala mafi yawan cinikayyar ƴan wasan da suka shigo ƙungiyoyinsu, sannan Spain da Portugal suka biyo bayan Premier League.

    Ƙungiyoyin Faransa ne suka samu mafi yawan kuɗin shiga daga cinikin ƴan wasan, inda suka karɓi dala biliyan 1.7 na Amurka (fan biliyan 1.25), sai na Ingila (fan biliyan 1), Jamus (fan miliyan 725), Spain (fan miliyan 571) da Portugal (fan miliyan 474).

    Ƙungiyoyin Ingila kuma sun jagoranci yawan cinikin ƴan wasa 512 da suka shigo ƙungiyoyi (an samu raguwar kashi 4.1) da kuma guda 596 da suka bar ƙungiyoyinsa a Premier League (ƙarin kashi 4.6).

  14. An kashe sama da dala biliyan uku ga ƴan wasan da suka buga kofin duniya a kasuwar cinikayya, Gasar kofin duniya

    An kashe sama da dala biliyan 3.3 wajen cinikin ƴan wasan da suka taka leda a gasar Kofin Duniya ta 2026, kamar yadda Fifa ta sanar bayan da aka rufe kasuwar cinikin ƴan wasa ta bazara.

    Fiye da ƴan wasan da suka buga Kofin Duniya su 260 daga ƙasashe 47 suka sauya ƙungiyoyi a lokacin kasuwar cinikayyar, lamarin da ya kai sama da kashi ɗaya cikin uku na adadin dala biliyan 9.89 da aka kashe, wanda ya zama tarihi, a ywan kuɗin saye da sayar da ƴan wasa tsakanin ƙasashe a ƙwallon ƙafar a cewar hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya.

    Wannan yawan kashe kuɗin ya biyo bayan nasarar da Spain ta samu wajen lashe Kofin Duniya a watan Yuli, abin da ya nuna yadda bajintar ƴan wasa a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya ta taimaka wajen haifar da kashe kuɗi mafi yawa a kasuwar cinikayyar duniya.

    Wasu fitattun ƴan wasan da suka haska a Kofin Duniya sun samu su sauya ƙungiya kan kuɗi da tsadar kuɗi a lokacin cinikayyar, ciki har da ɗan wasan Spain, Rodri, wanda ya koma Barcelona daga Manchester City, da kuma ɗan wasan Faransa, Bradley Barcola, wanda ya sauya sheƙa daga Paris St Germain zuwa Liverpool.

  15. Za a tsayar da wasannin lik a Argentina don karrama Messi, Lionel Messi

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina za ta karrama Lionel Messi bayan da ya yi ritaya daga buga wa ƙasar wasa ta hanyar dakatar da dukkan wasanninta a minti na 10 a wannan ƙarshen mako domin yin tafi na minti guda.

    Messi mai shekara 39, wanda ya sanya riga mai lamba 10 ta Argentina, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasa wasanni a ranar Litinin.

    Wasan ƙarshe da wanda ya lashe Ballon d'Or sau takwas ya buga wa ƙasarsa, shi ne wasan ƙarshe a Kofin Duniya a 2026, inda suka sha kashi a hannun Spain a watan Yuli. Haka kuma Messi ya jagoranci kasar zuwa lashe Kofin Duniya a Qatar a 2022 a matsayin kyaftin,

    "Hukumar Kwallon Kafa ta Argentina ta ce, domin girmamawa da karrama tarihin Lionel Messi tare da tawagar Argentina, a minti na 10 a dukkan wasannin lik ɗin kasar, alkalai za su dakatar da wasan kuma za a yi tafi na tsawon minti guda, domin karrana ɗan ƙwallon."

    Messi, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi bugawa Argentina wasa guda 207, ya taba yin ritaya daga buga wa ƙasa tamaula a 2016 kafin daga baya ya soke wannan shawarar.

    Hakan ya biyo bayan shan kashi da suka yi a hannun Chile a wasan ƙarshe a Copa America, inda ya kasa cin fenariti a karawar, yayin da Argentina ta sha kashi a wasan ƙarshe a manyan gasa karo na huɗu cikin shekaru tara.

    Tsohon ɗan wasan Barcelona ya ci gaba da lashe Kofin Duniya da kofunan Copa America guda biyu tare da Argentina, inda ya ci ƙwallo 125, mafi yawa a tarihin ƙasar.

    Messi ya fara bugawa tawagar ƙasar wasa a 2005 lokacin da ya shiga daga benci a minti na 63 ya yi canii a wasan sada zumunci da Hungary wanda Argentina ta yi nasara da ci 2-1.

    Tun bayan da ya koma makarantar horas da matasa ta La Masia ta Barcelona yana ɗan shekara 13, Messi bai taɓa buga wata babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa a ƙasarsa ta haihuwa ba.

    Shi ne na biyu a jerin waɗanda suka fi cin ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya da 21 a raga, bayan Kylian Mbappe na Faransa mai 22, sannan shi ne na biyu a yawan cin ƙwallayen a dukkan wasannin ƙasa da ƙasa mai 125 a raga, bayan babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo na Portugal mai 146.

    A watan Agusta, ya ce yana nazarin makomarsa a harkar ƙwallon ƙafa, bayan rasuwar mahaifinsa Jorge, wanda ya rasu yana da shekara 68 bayan doguwar jinya.

    Zai ci gaba da buga wasa a Major League Soccer tare da Inter Miami, inda yake da kwantiragin da zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta 2028.

  16. Trabzonspor ta sauya matsayi ta amince da murabus din kocinta, Trabzonspor

    Ƙungiyar Trabzonspor ta amince da murabus din da ta bayyana a matsayin na “yanayin da ya ɗaga mata hankali” daga babban kocinta, Fatih Tekke, bayan da kungiyar Turkiyya ta fara kin amincewa da bukatarsa ta sauka daga mukamin.

    Tekke, wanda ya jagoranci Trabzonspor zuwa matsayi na uku a gasar lig a kakar da ta gabata, ya mika takadar murabus dinsa bayan an fitar da kungiyarsa daga zagayen neman gurbin shiga Europa League da jimillar kwallaye 5-0 a hannun kungiyar Ferencvaros ta Hungary.

    Bayan kin amincewa da bukatarsa a ranar Juma’a tare da nuna cewa mai shekara 48 din ya yanke shawarar ne a lokacin da yake “tsananin ɓacin rai” sakamakon fita daga Europa League da kungiyar Super Lig din ta yi, yanzu ta amince da raba gari da babban kocinta.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, Trabzonspor ta ce ta cimma “fahimtar juna” da Tekke kuma ta yanke shawarar raba gari da shi “bisa maslahar Trabzonspor da manufofinta na dogon lokaci”.

    Sanarwar ta kara da cewa: “A tsawon kusan watanni 18 da ya yi a mukaminsa, Fatih Tekke ya kawo gagarumar gudummawa ga Trabzonspor.”

  17. Tottenham ta kashe fam miliyan 350 wajen sayen ƴan wasa, Tottenham

    Ƙungiyar Tottenham ta ɗauki ƴan wasa da yawa a bazarar nan, domin kara karfin ƙungiyar da ta sha da ƙyar a bara a ranar karshe a Premier League da tuni tana buga Championship a bana.

    Sai dai kuma kungiyar da Roberto De Zerbi da ke jan ragama ta buga wasa biyu da fara kakar nan ba tare da nasara ba a Premier League ta bana da aka fara a cikin watan Agusta.

    Ƴanwasan da Tottenham ta ɗauka kawo yanzu

    • Sandro Tonali (Newcastle) – fam miliyan 100
    • Savio (Manchester City) – fam miliyan 85
    • Mateus Fernandes (West Ham) – fam miliyan 85
    • Omar Marmoush (Manchester City) – aro tare da wajibcin saya kan fam miliyan 60
    • Jan Paul van Hecke (Brighton) – fam miliyan 52
    • Tosin Adarabioyo (Chelsea) – fam miliyan 7
    • Mykhailo Mudryk (Chelsea) – aro tare da zabin saya kan fam miliyan 75
    • Andy Robertson (kyauta)
    • Marcos Senesi (kyauta)
    • Martin Dubravka (kyauta)

    Ƴan ƙwallon da suka bar kungiyar a bazara

    • Luka Vuskovic (Brighton) – fam miliyan 50
    • Cristian Romero (Atletico) – fam miliyan 34.2
    • Djed Spence (Inter Milan) – fam miliyan 30
    • Kevin Danso (Sunderland) – aro tare da wajibcin saya kan fam miliyan 22.5
    • Radu Dragusin (Fiorentina) – aro tare da wajibcin saya kan fam miliyan 21.4
    • Will Lankshear (Middlesbrough) – fam miliyan 20
    • Ashley Phillips (Middlesbrough) – fam miliyan 20
    • Manor Solomon (West Ham) – fam miliyan 7
    • Pape Sarr (Juventus) – aro tare da zabin saya kan fam miliyan 25.7
    • Mikey Moore (Cologne) – aro
  18. Ƴanwasan da Liverpool ta ɗauka da waɗanda suka bar ƙungiyar

    Liverpool ta ɗauki ƴanwasa a bazarar nan, domin karfafa ƙungiyar a kakar bana, musammam maye gurbin Mohamed Salah, wanda ya bar Anfield a karshen kakar da ta wuce.

    Tuni ƙungiyar ta sayi Bradley Barcola da Victor Munoz a karkashin jagorancin sabon kociya, Andoni Iraola..

    Ga jerin ƴan wasan da ta ɗauka

    • Bradley Barcola (Paris St Germain) – fam miliyan 120
    • Jeremy Jacquet (Lille) – fam miliyan 60
    • Victor Munoz (Osasuna) – fam miliyan 34.5
    • Ronald Araujo (Barcelona) – aro

    Ga jerin ƴan ƙwallon da suka bar ƙungiyar

    'Yan wasan da suka bar kungiyar a bazara

    • Mohamed Salah (Trabzonspor) – kyauta
    • Ibrahima Konate (Real Madrid) – kyauta
    • Andy Robertson (Tottenham) – kyauta
    • Curtis Jones (Inter Milan) – fam miliyan 30
    • Harvey Elliott (Valencia) – aro
  19. Golan Chelsea, Sanchez, ya koma Como a matsayin aro

    Mai tsaron ragar Chelsea, Robert Sanchez, ya koma Como a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda bayan ya rasa matsayinsa na mai tsaron raga na farko ga Emiliano Martinez.

    Sanchez ne ya fara wasan da Chelsea ta doke Fulham da ci 3-2 a wasansu na farko a gasar Premier, amma ya bari ƙwallon da Josh King ya buga ta kuɓuce masa a kusurwar raga.

    Damuwa game da yadda dan kasar Spain din ke taka leda ta sa ƙungiyar ta Xabi Alonso ɗauko ɗan ƙasar Argentina, Martinez, daga Aston Villa kan kuɗi £7.5m.

    Martinez ne ya fara wasan da Chelsea ta doke Brighton da ci 4-3 a ranar Lahadi — sa'o'i kaɗan bayan ƙungiyar ta sanar da ɗaukarsa — yayin da aka cire Sanchez daga cikin jerin ƴan wasan da za su buga wasan.

    Sanchez, wanda ya kasance zaɓin farko a matsayin mai tsaron ragar Chelsea tun bayan komawarsa daga Brighton a shekarar 2023, ya buga wasanni 112 kuma ya lashe gasar Conference League da kuma Club World Cup tare da ƙungiyar ta Stamford Bridge.

    BBC Sport ta samu labarin cewa kungiyar Como, wadda tsohon ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Spain, Cesc Fabregas, ke horaswa, tana da damar sayen ɗan wasan mai shekaru 28 bayan ƙarewar wa'adin aron.

  20. Tottenham ta ɗauki aron Mudryk daga Chelsea

    Tottenham ta ɗauki ɗan wasan gefe na Chelsea, Mykhailo Mudryk, a matsayin aro har zuwa ƙarshen kakar wasa.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, ƙungiyar ta Spurs tana da damar mayar da zaman ɗan wasan na Ukraine mai shekara 25 zuwa dindindin kan kuɗi £75m.

    Wannan matakin ya sake haɗa shi da kociyan Spurs, Roberto de Zerbi, wanda ya taɓa horas da shi a ƙungiyar Shakhtar Donetsk kafin ya koma Chelsea a shekarar 2023.

    Mudryk ya warware batun shan kwayoyi masu ƙara kuzari da Hukumar ƙwallon ƙafa a watan da ya gabata, amma bai buga wasa ba tun watan Nuwamban 2024.

    Mudryk shi ne ɗan wasa na tara da Spurs ta saya a wannan bazarar inda ta kashe sama da fam miliyan 300 wajen cefanen ƴan wasa.

    Ana kuma sa ran Tottenham za ta kammala sayen ɗan wasan baya na Chelsea Tosin Adarabioyo ka kwantiragin dindindin kafin rufe kasuwar bazarar nan.