Dalilin da ya sa jam’iyyun siyasa 7 suka ƙulla ƙawance a Afrika ta Kudu domin ƙalubalantar ANC

Gamayyar jam'iyyun siyasar Afrika ta Kudu

Asalin hoton, Multiparty Coalition tweeter

Bayanan hoto, Gamayyar jam'iyyun siyasar Afrika ta Kudu
An wallafa

Jam’iyyun siyasa 7 a kasar Afrika ta Kudu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta haifar da babban kalubale ga jamiyyar ANC mai mulki a zaben 2024.

Gamayyar jam’iyyun da ake kira Multi-Party Charter for South Africa sun cimma matsaya kan yadda za su yi aiki, tare da raba mukaman ministoci da kujerun ‘yan majalisa idan sun hau mulki.

'Yan siyasar sun tattauna a wani babban taron kwanaki biyu da aka yi a Kempton Park da ke gabashin Johannesburg.

Jam’iyyun siyasar kasar Afrika ta kudu sun kula kawance ne domin karbe mulki daga jam’iyyar ANC mai mulki tare da hana jam’iyyar Economic Freedom Fighters ta Julius Malema damar samun galaba a zaben.

Gammayar jam’iyyun siyasar nada anniyar bunkasa tattalin arzikin kasar da ke fuskantar komabaya tare da kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa da daukewar wutar lantarki.

Sun kuma amince da cewa jam’iyyar da ta fi samun kuri’u a babban zaben da za a yi a badi ita ce za ta jagoranci harkokin kasuwanci na gwamnati kuma ita ce za ta bada wanda za a nada a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Sai dai jam’iyyun siyasar ba su yanke shawara kan wanda za a zaba a matsayin shugaban kasa ba idan sun yi nasara a yunkurinsu na karbar mulki.

Jam’iyyun sun kuma amince cewa za a gudanar da bincike domin tantance yadda mambobin zartaswa ke rayuwa.

Masu sharhi sun ce kafuwar gammayar jam’iyyun ka iya zama barazana ga jam’iyyar ANC mai mulki wadda a shekarun baya baya nan ta rika samun raguwa a rinjayen da ta ke shi.