Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zan fi bai wa ilimi muhimmanci a Kebbi idan na samu nasara – Dan takarar gwamna na NNPP
Zan fi bai wa ilimi muhimmanci a Kebbi idan na samu nasara – Dan takarar gwamna na NNPP
An wallafa
Dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP a jihar Kebbi, Nasir Abubakar ya ce zai fi mayar da hankali ga fannin ilimi musamman na firamare da na sakandare.
Ya ce tun kafa jihar Kebbi kawo yanzu, al’ummar jihar ba su samu abin da suke so ba daga gwamnatocin kasancewar ba al’ummar ne a gabansu ba.
Ya kara da cewa zai kuma tabbatar da bayan ilimin na bai wa jama’a horo na musamman a makarantu ta yadda idan sun gama za su iya dogaro da kansu.