Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ya kamata mutane su rage dogon buri kan Pi'
'Ya kamata mutane su rage dogon buri kan Pi'
An wallafa
Wani masani kan harkokin kudaden kirifto ya yi kira ga mutanen da suke harkar kudaden na intanet da su rage dogon buri.
Adamu Abubakar ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa.
Ya kara da cewa ya yi kiran ne domin kada masu yin wannan harkar su fuskanci karayar zuciya idan ba su samu biyan bukata ba.
A cewarsa, harkar kirifto ba ta da tabbas sannan ana karbar bayanan jama'a da ba su san abin da za a yi da su ba.