Likitan da aka tursasa wa yaƙar masu masu iƙirarin jihadi

Asalin hoton, Arouna Louré
- Marubuci, Khadidiatou Cissé
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
A cikin watan Satumbar, 2023, Dr Arouna Louré na aiki a dakin tiyata a inda yake aiki a Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, a lokacin da sojoji dauke da makamai suka kutsa cikin dakin tiyatar.
"Sun fahimtar da ni za su iya bari na in bi su cikin lallama ko kuma su yi amfani da karfin tsiya" a cewar likitan mai shekaru 38.
"Wani likitan ne ya maye gurbina ya ci gaba da tiyatar da na ke, sannan mu kuma muka tafi."
Sojojin sun hankada Arouna Louré cikin wata mota, da aka tafi da ita zuwa sansanin horas da sojoji mai nisa. An kai shi wajen ne don yaki da masu ikirarin jihadi da ke daya daga cikin yanki mai matukar hadari.
Kwanaki kadan kafin dauke shi, Louré ya wallafa wani sako da ya ke sukar Burkin faso a shafinsa na sada zumunta, kan yadda sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, bayan da ya sami wasikar sanar da shi matakin tursasa shi shiga aikin sojan kasar.
"Kasa irin wannan, ba mu da 'yanci, fadin ra'ayinmu ko tunaninmu," in ji shi.
Louré na daya daga cikin maza 'yan Burkina Faso da aka tursasa musu shiga cikin dakarun kasar da ake kira Volunteers for the Defence of the Homeland (VDP), maza masu yawa da suka kalubalanci matakin gwamnatin.

Asalin hoton, Arouna Louré
Burkina Faso da Kremlin
Shugaban mulkin sojin a Burkina Faso Captain Ibrahim Traoré ya kwace mulki a kasar Satumbar, 2022, tuni ya mayar da hankali wajen kara karfafa dangantakar Rasha da Afrika.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Alhamis Traoré wanda shi ne shugaban kasar da ya fi kowane shugaban kasa nahiyar karancin shekaru ya tabbatar da cewar idan akwai bukata dakarun Rasha za su iya shiga sahun masu yaki da masu ikirarin jihadi a kasar, a mako guda bayan da Mascow ta jibge dakarunta guda 100 kasar.
Burkina Faso dai na cikin jerin kasashen da ke yankin Sahel, da aka yi juyin mulki a kasashe shida tun daga 2020: ga biyu a Mali, biyu a Burkina Faso, daya a Ghana, daya a Guinea.
Tun a 2015 kasar ke fuskantar rikici, a yankunan ta biyu. Kungiyoyin masu ikirarin jihadi da rikicin bayar da agaji na daga cikin abubuwa da ke kara taazzara talauci, da raba mutane da matsugunensu da rashin abinci.
Sai dai an sami karuwar fitar da gwal, yayin fitar da kayan amfanin gona, ya zama abin da ta fi dogara da shi, amma fiye da rabin yan kasar na fama da talauci, kamar dai yadda wani rahoton bankin duniya ya nuna.
A shekarar 2023 kadai, a cewar wani rahoton hukumar tattara bayanan inda ake rikici ko yaki ta ACLED, ta ce sama da mutum dubu shida ake zargin yan bindigar suka halaka.
Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta ce sama da yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a kasar ta Burkina Faso.

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da BBC ta tuntubi mai magana da yawun Ma'aikatar shari'a, don mayar da martani kan wannan batu, sai dai ba ta ce uffam ba kan lamarin.
Sai dai a cikin watan Nuwamba, a lokacin da aka tambaye su kan kalaman Traoré ya yi na "yancin yan kasa, bai fi yancin kasa ba", sannan ya kara da cewar "ba a gina kasa a kan rashin da'a da rashin tsari"
Idan mun koma watan Afrilu 2023, Traoré ya yi alkawarin inganta tsaron, saboda yadda ya tabarbare a kasar, cikin "wattani biyu zuwa uku da hawansa mulki," wajen mayar da hankali domin ganin mun yi nasara wajen kwato yankunan kasar da masu ikirarin jihadi suka kwace, tare da mayar da kasar mulkin farar hula a watan Yulin 2024.
Cikin wannan shirin ya ce karin fararen hula 50 za su dauka don shiga runduna ta musamman ta VDH.
A cikin watan Afrilun 2023, aka sanar da wani shiri na karbe yankunan da ke hannun masu ikirarin jihadi, tare da samar da wata doka da ta bai wa gwamnati tursasawa fararen hula yaki da masu ikirarin jihadi.
Sai dai bayan wasu watanni, tsaro ya sake tabarbarewar kuma haka ya sa Traoré ya dakatar da gudanar da zabe a kasar, yana mai cewar yanzu ba shi da matukar muhammanci, a halin da kasar ke ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Ana harin 'yan gwagwarmaya da 'yan adawa
Kungiyoyin kare hakkin Dan adam ta kasa da kasa Amnesty International, na ta neman hukumomin Burkina Faso da ta saki dan rajin kare hakkin dan adam Dr Daouda Diallo.
A wata sanarwa da Amensty International din ta fitar ta yi kira da " mika mulki ga farar hula, don kawo karshen tursasa yan kasar shiga soji, don rufe bakunan wadanda ke kalubalantar hakan.
Iyalan Diallo da lauyoyi na da yakinin cewar jami'an tsaro ne suka yi garkuwa da shi a 1 ga watan Disamba, bayan da ya bar ofishin fasfo a Ouagadougou. bayan wasu kwanaki wani hoto da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuno shi a bayan wata motar sojoji sanye da kayan soji.
ita ma kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, da ta Reporters Sans Frontières, sun ce akwai jerin yan rajin kare hakkin dan adam, yan jarida, da shugabanni 'yan adawa na daga cikin wadanda aka tursasawa shiga aikin sojan.
Ilaria Allegrozzi, wata babbar mai bincike ne a kungiyar ta human rights watch, ya ce halin da Burkina Faso ke ciki, " daya daga cikin munanan lokuta a tarihi" a bangaren kare hakkin dan adam, albarkacin fadar baki da dokin bayar da agaji na kasa da kasa.
"Amfani da tursasawa ba wai haramun ne ba kawai, rashin imani ne, saboda nufakar da ake zaba, da suka kalubalanci gwamnatin, in ji ta.
Allegrozzi ta yi bayanin cewar ya kamata idan za a yi amfani da tursasawa, a yi ta bisa tsari, ba tare da nuna banbanci da rashin nuna fifiko, da amfani da doka.
“Hukumomin Burkinabè na buga gangar halasta yaki, da masu ikirarin jihadi, amma a daya bangaren amfani da cin zarafi wajen yakar wani cin zarafin, ba zai taba zama daidai ba, in ji ta.

‘Ina cikin matsanancin tsoro kowane lokaci’
Nathalie (wadda muka sauya sunanta saboda tsaro) ta ce mijinta wanda dan jarida ne, na daya daga cikin wadanda aka kira a baya bayan nan. ma'auratan sun yi magana da BBC a sabon gidansu da ke kasar waje.
"Lamarin ya koma kamar ma ba ma rayuwa, a cewarta.
Danginta sun tsammaci martani daga binciken kwakwaf da mijinta yake yawan rahoto a kai, amma ya tsere daga kasar a lokacin da wasikar za ta zo gare shi.
Wani farar hula da aka tursasawa shiga soja, ya sanar da BBC cewar an shigar da su yaki da babu wani cikakken horo ba.
Louré ya sami dan horo na yaki, kafin a kai shi Kaya, d Ouahigouya, sannan Koumbri.
Suna daga cikin wuraren da ke da matukar hadari a kasar. An yi kiyasin cewar sojoji 17 da sojojin sa-kai 36 da ake zargin an hallaka a wani karon batta da aka samu a watan Satumba.

Asalin hoton, Getty Images
“Zamana a asibiti ya fi min amfani , kan shiga filin daga", in ji Lao Louré.
“A Zahirance ba ni da wani amfani. ina iya rike bindigata ba daidai ba, ko ma na iya harbin wani farar hula ko wani sojan", in ji shi.
Kungiyar da ke bincike kan rikice-rikice ta duniya (ICG) ta ce rashin cikakken horo ga rundunar ta VDP, barazana ce ga rayuwar fararen hula, da ke tsintar kansu a musayar wutar da ake yi.
A watan Disambar bara Kungoyin kare fararen hula a Burkina Faso cikin har da fitattun 'yan jarida da kungiyar 'yan adawa ta Le Balai Citoyen sun gurfanar da gwamnatin a gaban kotu kan shirinta na tursasawa yan kasar aikin soji.
Daya daga cikin Lauyoyinsu Guy Hervé Kam, ya ce gwamnati ta raba takardun gayyatar aikin soja ga wasu daga cikin mambobinta , jim kadan bayan da suka sanar da zanga-zanga a babban birnin kasar, don nuna adawarsu kan "shirin takaita 'yancin 'yan kasa".
Wata kotu ta bayyana tursasawar a matsayin haramtacciya, sannan ta umarci da a janye dokar. "Mun iya nuna cewar tursasawa mutane shiga soja, ba shi da amfani, kuma ana mayar da shi hanyar hukunta mutane", in ji Kam.
Sai dai gwamnatin da ta yi juyin mulki a kasar ta daukaka kara kan batun, kuma har yanzu batun na gaban kotun.

Asalin hoton, Getty Images
‘Munufar ita ce cin mutunci'
Nathalie ta yi fama da cutar damuwa inda ta gaza karbar tunanin za ta ma iya komaw gida.
“A duk lokacin da mijina ya fita, na kan tambayi kaina: ko zai dawo? Za a iya dauke shi? Ko kuwa wani zai kira ni a sanar da ni cewar shi ma an kai shi aikin soja? in ji ta.
Bayan wattani uku da fara aikin soja, Dr Arouna Louré ya dawo gida cikin iyalinsa.
Ya ce mutane irinsa da suka tsinci kansu a wajen, babu wata hanya da za ka iya fita ko guduwa.
"Manufar shirin dama shi ne a ci mutunci. Idan ka bi umarnin, za su dauki hotonka sannan su wallafa shi a kafafen sada zumunta don su ci maka mutunci. Idan ka tsere daga kasar, za su kira ka da matsoraci. Idan ka shigar da gwamnati kara sai su sanar da 'yan kasar kai matsoraci ne nan ma," ya kara da cewar.
Ya ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta sannan yana da karfin guiwar kan makomar kasar.
"Dabara da muka yi amfani ita ce yaki da cin hanci da rashawa, da haramtatun hanyoyi don azurta kai, da san kai. hakan ba ya faruwa a fagen daga, sai dai a babban birnin kasar, Ouagadougou,” inji shi.










