Arsenal na nazari kan Lookman, Chelsea na zawarcin Mainoo

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran Ademola Lookman zai bar Atalanta a wannan bazarar kuma ɗan wasan na Najeriya, mai shekara 27, a shirye yake ya koma gasar Premier inda rahotanni ke cewa Arsenal da Chelsea na sha'awarsa. (Teamtalk)
Chelsea na shirin ƙara ƙaimi wurin zawarcin ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 19, yayin da ake ƙara nuna shakku kan ƙoshin lafiyar ɗan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia, mai shekara 21. (CaughtOffside)
AC Milan na zawarcin ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Tyrick Mitchell, mai shekara 25, a bazara, yayin da ta ke shirin raba gari da ɗan wasan Faransa Theo Hernandez, mai shekara 27. (Teamtalk)
Ɗan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips, mai shekara 29, zai iya komawa Leeds a bazara bayan ya shafe wannan kakar wasan yana zaman aro a Ipswich. (Sun)
Arsenal na shirin fara zawarcin ɗan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, daga Newcastle. (Football Insider)
Manchester United na tunanin ɗaukar ɗan wasan Porto ɗan ƙasar Sifaniya Samu Aghehowa, mai shekara 20, wanda farashinsa ya kai £84m. (GiveMeSport)
Liverpool na tunanin ko za ta ɗauko ɗan wasan baya na Brighton ɗan ƙasar Netherlands Jan Paul van Hecke, mai shekara 24. (GiveMeSport).
Al-Riyadh da FC Dallas da Wolves suna cikin ƙungiyoyin da ke nuna sha'awa kan ɗan wasan bayan Ingila Michael Keane, mai shekara 32, wanda kwantiraginsa a Everton zai ƙare a wannan bazarar. (Mail)
Har yanzu Fikayo Tomori na AC Milan na ci gaba da kasancewa a kasuwa bayan da ya kusa komawa Juventus da Tottenham a watan Janairu, kuma mai tsaron bayan na Ingila na ɗauke da farashin kusan Yuro miliyan 20. (Calciomercato)
Ɗan wasan Brighton ɗan ƙasar Sweden Yasin Ayari, mai shekara 21, yana jan hankalin Borussia Dortmund da AC Milan. (Football Insider)
A wannan makon ne dakatarwar da aka yi wa Paul Pogba za ta ƙare amma duk da tayin da ake yi masa, tsohon ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 31, har yanzu bai yanke shawarar inda zai ci gaba da taka leda ba bayan ya bar Juventus. (L'Equipe)
Everton za ta nemi ta rage albashin ɗan wasan tsakiyar Mali Abdoulaye Doucoure a wani sabon kwantaragi bayan ta ƙi amincewa da batun tsawaita wa ɗan wasan mai shekaru 32 kwantiraginsa da shekara ɗaya. (Football Insider)











