Manyan matsalolin da ke gaban sabon shugaban Ghana

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Thomas Naadi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Tamale da Accra
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Sabon shugaban Ghana da aka rantsar, John Mahama, zai fuskanci matsi wajen magance matsalolin da suka sanya al'umma suka kaɗa masa ƙuri'a da gagarumin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasar na watan Disamba.
Ya koma kan muƙamin bayan kwashe shekara takwas yana adawa, bayan ya aiwatar da kamfe "cikin ƙwarewa" kamar yadda mai nazari kan siyasar ƙasar, Nansata Yakubu ya bayyana.
Ya kayar da mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia da kashi 56.6 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Mista Bawumia ya samu kashi 41.6 cikin 100, inda hakan ya zama tazara mafi girma tsakanin 'yan takara cikin shekara 24.
To sai dai an samu raguwar fitowar masu zaɓe idan aka kwatanta da zaɓen 2020, musamman a wuraren da jam'iyyar Bawumia ta NPP ke da ƙarfi, abin da ake alaƙantawa da yadda mutane suka yanke ƙauna da ƙoƙarin jam'iyyar na inganta al'amura a ƙasar.
Yayin da ƙurar siyasa ke lafawa bayan rantsar da sabon shugaban ƙasar, Belinda Amuzu - wata malamar makaranta a birnin Tamale da ke arewacin ƙasar, inda Mahama ke da ƙarfi - na ɗari-ɗari kan makomar ƙasar.
"Ina fatan sabuwar gwamnatin za ta zo da sauye-sauyen tattalin arziki, domin sauƙaƙa wa al'umma. Ya kamata kuma ya gurfanar da jami'an gwamnati da aka zarga da cin hanci, domin koya wa saura darasi,'' kamar yadda ta bayyana wa BBC.
"Matsin rayuwa" ya zama ruwan dare a Ghana. Tun lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga mawuyacin hali a 2022, tare da haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki, lamarin da ya shafi farin jinin Mawumia a matsayinsa na ''ƙwarare kan fannin tattalin arziki'' - har ya janyo masa shan kaye a hannun Mahama.
Farfesa Godfred Bokpin, wani ƙwararren masanin tattalin arzikin ƙasar, ya shaida wa BBC cewa ƙalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin na da yawan gaske.
"Abin da Ghana ke so yanzu shi ne shugabanci nagari da gwamnati mai tsafta don gudanar da aiki ga 'yan ƙasa. Idan ba a samu wannan ba, to an kauce layi," in ji shi.
Mahama ya kuma alƙawarta rage adadin ministocin gwamnati daga fiye da 80 zuwa kusan 60, to amma Farfesa Bokpin ya ce ya kamata a ce adadin ya yi ƙasa da hakan, yayin da Dakta Kwame Asah-Asante Yakubu ke ganin cewa ya kamata a bi ƙa'ida wajen naɗa muƙaman, maimakon waɗanda ke yi masa biyayya.
Mahama zai yi aiki tare da tsohuwar ministar ilimin kasar, Naana Jane Opoku-Agyemang, wadda za ta kasance mace ta farko da ta riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban ƙasa, idan aka rantsar da su a watan gobe.
Dakta Kwame ta ce an naɗa ta muƙamin ne ba don alfarma ko "daɗaɗa" mata ba, kuma ita ba mace ba ce da za a iya ''juyawa'' ba.
"Mataimakiyar shugaban ƙasar na da ƙwarewar aiki,'' kamar yadda Dakta Kwame ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mahama ya yi wa'adin farko na shekara huɗu a matsayin shugaban ƙasa bayan ya yi nasara a zaɓen 2012, amma ya sha kaye a koƙarinsa na zarcewa a wa'adi na biyu a 2016, inda Nana Akufo-Addo ya samu nasara tare da Bawumia a matsayin mataimaki.
Dakta Kwame ta ce Mahama ya tsaya tsaya takara a 2016 ne domin ci gaba da aikin tarihi da ya faro na gina tituna da asibitoci amma masu zaɓe suka yi watsi da shi, bisa tunaninsa a lokacin na cewa ''ai ba aiki ba za mu ci'.
To amma masaniyar tattalin arzikin ta ce a lokacin annobar Covid al'ummar Ghana sun yaba wa Mahama kan gine-ginen da yayi musamman asibitoci.
Musamman a lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga halin tsaka mai wuya karƙashin gwamnatin Afuko-Addo, abin da tilasta mata karɓo rancen dala biliyan uku daga wurin Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, wannan abu ya taimaka wajen sake zaɓar Mahama, in ji Dakta Kwame.
Ta shaida wa BBC cewa a yanzu ana sa ran Mahama zai cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman samar da ayyukan yi, domin rage adadin masu zaman kashe wando da kusan kashi 15 cikin 100, da kuma rage tsadar rayuwa ta hanyar soke wasu haraje-haraje - ko abin da 'yan ƙasar suka kira ''haraje-haren da ake kokawa a kansu''.
Mahama ya alƙawarta inganta tattalin arzikin ƙasar, ta hanyar ɓullo da ayyukan dare yi a ma'aikatun gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu. Ya ƙara da cewa zai bai wa 'yan kasuwa tallafi domin su ci gaba da wanzuwa har cikin dare da kuma rage musu kuɗin wutar lantarki.
To sai dai masu suka na da shakku game da batun, inda suke nuni da matsalar lantarki, da aka shiga a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.
Ya kuma alƙawarta soke haraje-haraje masu yawa ciki har da harajin tura kuɗi ta waya da ya fi shan suka tsakanin 'yan ƙasar da kuma hayaƙin carbon da motoci masu mafani da lantarki ko man disel ke fitarwa.
Farfesa Bokpin ya ce yana shakku idan gwamnatin Mahama za ta iya cika alƙawuran da ta ɗauka.
"Ba su yi nazarin abin da alaƙawuran nasu za su laƙume ba. babu wadatattun kuɗin da za su aiwatar da alƙawuran nasu,'' in ji shi.
To amma Mahama na da ƙwarin gwiwar bai wa masu shakkun mamaki, inda ya ce zai sake nazarin yarjejeniyar bashin da ke tsakanin ƙasar da IMF domin yafe wa ƙasar wasu ɓangaren kuɗin'', da kuma gudanar da shirye-shiryen tallafa wa talakawa a ƙasar da mutum miliyan 7.3 ke rayuwa cikin talauci.
A wata hira da ya yi da BBC gabanin zaɓen, Mahama ya ce IMF na buƙatar wani adadi na kuɗi daga cikin kuɗaden gwamnati.
"Idan ka samu nasarar rage kashe kuɗaɗen gwamnati sannan ka ƙara kuɗin shiga da ba na haraji ba, za ka iya shawo kan matsalar'', in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Dakta Asah-Asante ta ce riƙe muƙamin shugaban ƙasar da Mahama ya yi a baya, zai ba shi damar magance matsalolin da ƙasar ke fama da su.
"Tabbas zai iya fuskantar matsaloli, amma yana da ƙwarewar da zai iya magnace su,'' in ji mai sharhin.
Bayan tattalin arziki, cin hanci da rashawa na ɗaya daga cikin matsalolin da Ghana ke fuskanta, amma ba kowa ne yake da yaƙin cewa Mahama zai magance matsalar ba.
Gwamnatocin Mahama da suka gabata na muƙamin shugaban ƙasa da mataimaki sun sha fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa, kodayake ya sha musanta aikata laifi.
A shekarar 2020, Kotun Birtaniya ta samu fitaccen kamfanin jiragen sama na Airbus da bayar da rashawa domin samun kwangila da Ghana wajen sayen jiragen soji tsakanin 2009 zuwa 2015.
An fara binciken ne a Ghana, amma ofishin mai shigar da kara na musamman a wani mataki da aka bayyana watanni kafin zaɓen, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa akwai hannun Mahama a ayyukan rashawar.

Haka ita ma gwamnati mai karewa ta sha fuskantar zarge-zargen rashawa, ciki har da badaƙalar sayen kayan gyaran motocin ɗaukar masara lafiya da ya laƙume dala miliyan 34.9 da kuma batun aikin gina cocin ƙasa inda aka kshe dala miliyan 58 ba tare da ganin wani gagarumin ci gaba a aikin ba.
Mahama ya alƙawarta cewa gwamnatinsa za ta magance matsalar cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da cewa an gurfanar da jami'an gwamnati da aka samu da laifi.
"Muna tunanin kafa kotuna na musamman," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Dakta Asah-Asante ta ce ya kamata Mahama ya buƙaci cikakkun bayanai daga gwamnati mai ƙarewa a lokacin shirye-shiryen miƙa mulki, ''don haka idan akwai wanda ya aikata ba daidai ba, sai ya gyara'', da zarar gwamnatinsa ta kama aiki.
Mai sharhin ya ce Mahama ba shi da zaɓi face cika wa 'yan Ghana fatansu, ko kuma su hukunta gwamnatinsa kamar yadda suka hukunta gwamnatin NPP.
Mahama ya amince da wannan a jawabinsa na karɓar mulki, inda ya ce ''fatan 'yan Ghana na da yawa, kuma ba za su amince ya kunyata fatan nasu ba.
"Akwai alamun cewa muna da makoma mai kyau a gaba. Gaba za mu riƙa yi har abada ba baya ba."












