Za a yi wa ɗan Najeriya afuwa bayan yanke masa hukuncin kisa kan satar kaji

    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kano
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Wani ɗan Najeriya da ya shafe shekaru 10 a gidan yari yana jiran a zartar masa da hukuncin kisa saboda satar kaji, zai shaƙi iskar 'yancin bayan da gwamnan jihar Osun ya yi alƙawarin yi masa afuwa.

Segun Olowookere na da shekara 17 a shekara ta 2010 lokacin da aka kama shi tare da wani mutumin da suka haɗa baki mai suna,Morakinyo Sunday.

Ana zargin su da kai hari a gidan wani ɗansanda da kuma gidan wani farar hula riƙe da tsohuwar bindigar harba ka ɓoye da kuma wata adda inda suka yi sata a gidan gona.

A shekara ta 2014, Mai shari'a Jide Falola na babbar kotun jiha da ke Osun ya yanke wa mutanen biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ya same su da laifin ɓalla gidan wani ɗan sanda tare da yi masa sata.

Lamarin ya ja hankali sosai a Najeriya a wancan lokacin inda mutane ke cewa hukuncin ya yi tsanani sosai.

Daga bisani mutanen biyu an kai su gidan yarin Kirikiri da ke jihar Legas inda aka ajiye su a ɓangaren masu jiran a aiwatar musu da hukuncin kisa.

A wata sanarwa a ranar Talata, gwamna Ademola Adeleke ya bayar da umurni a yi wa Olowookere afuwa.

"Na bayar da umurnin kwamishinan shari'a ya soma aiki domin yin afuwa ga wannan matashin.

"Osun jiha ce ta adalci da daidaito. Dole ne mu tabbatar da adalci da kuma kare rayukan al'umma," gwamnan ya rubuta a shafinsa na X.

Sai dai ba a san makomar Morakinyo Sunday ba, wanda tare aka yanke musu hukuncin kisa da Olowookere saboda ba a ambato sunansa a sanarwar ba.

A tsawon shekaru, iyayen Olowookere da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da kuma 'yan Najeriya sun yi ta fafutukar ganin an sako shi.

Iyayensa sun bayyana cewa shi ne kaɗai ɗansu kuma ya kamata a yi masa afuwa.

Ana sa ran sakin sa a farkon shekara ta 2025.

Rabon da a aiwatar da hukuncin kisa a Najeriya tun shekara ta 2012, amma kuma a yanzu haka akwai mutane fiye da 3,400 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisan.