An taɓa hanani aure saboda ni mawaƙi ne - Sammanin Waƙa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
An taɓa hanani aure saboda ni mawaƙi ne - Sammanin Waƙa
An wallafa

Matashin mawaƙin da ke fafutikar ganin masu basirar waƙa irinsa sun ƙirƙiro waƙoƙinsu ba kwaikwayo ba.

Sammani A.A ya ce ya fara waƙa ne a shekarar 2019, ya kuma rera waƙoƙi masu yawa tun lokacin.

Sammanin waƙa, kamar yadda aka fi saninsa, ya ce kullum a Nura M Inuwa ne madubinsa a fagen waƙa.

Matashin mai shekara 27 ya ce babban ƙalubalen da yake fuskanta, shi ne kasancewarsa mawaƙi, saboda idan ya je neman aure yakan fuskanci matsala