Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyoyin Saudiyya na shirin ɗauke De Bruyne, Arsenal za ta dawo da Marquinhos
Manchester City ta sanya wa ɗan wasan tsakiyar Ingila, Kalvin Phillips farashin £50m inda ta ƙudiri aniyar cin riba kan ɗan shekara 27 ɗin da ta ɗauko daga Leeds United a kan £42m a 2022. (Mirror)
Ƙungiyoyin Saudiyya na shirin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Belgium, Kevin De Bruyne, a 2024, inda suka yi mashi tayin albashi mai tsoka. (Football Insider)
Kociyan Arsenal, Mikel Arteta na fatan samun ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad da Sifaniya, Martin Zubimendi, yayin da kuma yake bibiyar ɗan wasan Real Madrid da Faransa, Aurelien Tchouameni. (Mirror)
Tottenham na zawarcin ɗan wasan Borussia Monchengladbach da Japan, Ko Itakura. (Fichajes - in Spanish)
Dan wasan tsakiyar Al-Hilal, Ruben Neves, na fatan komawa taka leda a Newcastle United, a watan Janairun baɗi. (O Jogo, via Sporting Witness)
Manchester City da Liverpool na bibiyar ɗan wasan Bayern Munich mai shekara 20, Jamal Musiala, wanda ke neman canza ƙungiya a watan Janairu. (Football Insider)
Aresenal za ta duba yiyuwar dawo da ɗan wasanta da ke zaman aro a Nantes, Marquinhos, a watan Janairu. (Mirror)
Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen, ya yi watsi da rahoton barin Napoli, inda aka alaƙanta ɗan shekara 24 ɗin da manyan ƙungiyin Ingila, ciki harda Liverpool. (Mirror)