Yadda aka gabatar da bikin karrama gwarzan gasar rubutu ta matasa a Kano
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ce ta shirya gasar gajerun labarai ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abba El-Mustapha, a karon farko a 2024.
An dai bayyana matashi Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda ya zo na farko a gasar gajerun labaran.
Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa kan yadda gasar ta gudana tare da taya wanda suka yi nasara murna.
Zubairu Musa Balannaji wanda ya lashe gasar ya gode wa Allah ya yi tare nuna farin cikinsa dangane da wannan gagarumar nasarar da labarinsa ya samu.






