Waiwaye: Ƙurar da ziyarar Tinubu a Katsina ta tayar da haramta yaɗa shirye-shiryen siyasa kai-tsaye a Kano

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku bitar muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

Ziyarar Tinubu da ta turnuƙe Katsina da ƙura

An shiga makon da ce-ce-ku-ce kan ziyarar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyara, wanda har Gwamna Umar Dikko Raɗɗa na jiyar ya fitar da jawabi a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure game da ziyarar ta kwana biyu a jihar wadda ɗaya ce cikin jihohin Arewa maso Yamma da suka fi fama da masifar rikicin 'yan fashin daji.

Ka-ce-na-ce ya ɓarke ne har a shafukan sada zumunta tun lokacin da aka fara ganin wasu manyan allunan da aka kakkafa ɗauke da saƙon 'Katsina Ba Ƙorafi', a yayin ziyarar.

Saƙon 'Katsina Ba Ƙorafi' ga alama ya jefa ɗumbin mutane cikin mamaki, inda suke neman sanin hikimar nuna wa Tinubu cewa jihar ba ta da wani ƙorafi, duk da a zahiri, ba gaskiya ba ne.

Yadda ake zargin amarya ta yi wa angonta yankan rago a Kano

Haka kuma a makon ne rundanar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wata amarya da ake zargi da halaka angonta a ranar Talata.

Cikin wata sanarwa, rundunar ta ce tana zargin amaryar mai suna Saudat Jibril 'yar shekara 18 ta halaka angonta Salisu Idris mai shekara 30 ne ta hanyar yi masa yankan rago da wata wuƙa mai kaifi.

Mai magana da yawun rundunar ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Farawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a arewa maso yammacin Najeriya.

"Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:35 na dare a ranar 6 ga watan Mayun da muke ciki, inda wadda ake zargi wato amryar ta yanka mijin nata da wata wuƙa mai kaifi", in ji SP Kiyawa.

Lamarin ya harzuƙa mazauna Kano da arewacin Najeriya, musamman a shafukan sada zumunta, inda mutane ke bayyana alhini.

Shin 'yan bindiga sun ɓulla jihar Bauchi ne?

A cikin makon ne dai aka wayi gari da labarin kisan da 'yan bindiga suka yi wa wasu 'yan banga ko 'yan sa-kai a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya jawo tambayoyi da kuma damuwa game da yadda ayyukan masu ɗauke da makamai ke faɗaɗa a arewacin ƙasar.

A ranar Litinin da dare ne rundunar yan sanda a jihar ta Bauchi ta tabbatar wa BBC kisan da 'yan bindiga suka yi wa wasu 'yan sintiri sakamakon wani kwanton ɓauna da suka yi wa yan sintirin ranar Asabar a dajin Madam da ke kusa da iyakar Bauchi da jihar Filato.

Artabun ya faru ne a lokacin da jami'an tsaro na sa-kai da ake wa lakabi da "Professional Hunters" suka gamu da 'yan bindigar a ƙauyen Mansur, in ji mai magana da yawun rundunar CSP Ahmed Muhammad Wakili.

Ya ce da ma garin na Mansur mai iyaka da Taraba, da Filato da Gombe wuri ne da ke fama da matsalar ɓarayin daji.

Ko gwamnatin jiha a Najeriya na da ikon yi wa gidajen rediyo iyaka?

Wani al'amari da ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane a makon shi ne matakin gwamnatin jihar Kano ya neman a daina yaɗa shirye-shiryen siyasa kai-tsaye a jihar.

Hakan ya sa wasu suka riƙa tambayar ko gwamnatin jiha na da ikon ɗaukar irin wannan matakin.

Sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Najeriya, na 1999 ya yi tanadin cewa, dole ne kodayaushe kafafen yaɗa labarai da suka hada da gidajen rediyo da talabijin da sauransu, su kasance masu 'yancin kiyaye muhimman manufofin ƴancin faɗin albarkacin baki.

Sashen ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai ƴancin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Haka kuma sashen ya kare ƴancin faɗin albarkacin baki, tare da tabbatar da cewa kowane mutum na da damar bayayana ra'ayinsa ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Dakta Sulaiman Santuraki, malami a makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya da ke Yola, ya ce akwai wasu wurare da gwamnatin jiha ke da hurumin taka wa gidajen rediyo birki.

Gwamnatin je-ka-na-yi-ka a Najeriya

A wani labarin kuma da aka yi ta muhawararsa a makon, jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta mayar da martani game da wata gwamnatin je-ka-na-yi-ka da wasu 'yan adawar siyasa suka kafa, da nufin kalubalanta da yin gyara ga manufofin gwamnatin kasar.

Matakin da jam'iyyar ta ce bai girgiza ta ko daga mata hankali ba, domin kuwa mataki ne na bigi-bagiro kawai, wato tamkar wani hotoho ne kawai.

Sai dai masana na ganin wannan gwamnatin ta je-ka-na-yi-ka, wadda akan yi irin ta a wasu kasashe, za ta wata sabuwar hanyar zaburar da gwamnatin kasa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al'umma.

Martanin na jam'iyar APC mai mulkin Najeriya, yana zuwa bayan da wani fitaccen masanin tattalin arziki, kuma dan gwagwarmayar siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi ya bude wani sabon shafin salon hamayyar siyasa a kasar, ta hanyar kafa gwamnatin je-ka-na-yi-ka.

Zargin mayar da Najeriya tsarin jam'iyya guda?

Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al'amuran siyasa, a cikin makon ne tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa "abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam'iyya guda ɗaya".

Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al'amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana.

Amma a makon ne tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam'iyya guda.