Man City na zawarcin Destiny Udogie, Ina makomar Lookman a Atalanta?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta sanya sunan ɗanwasan Tottenham da Italiya Destiny Udogie mai shekara 22 cikin jerin waɗanda za ta iya ɗauka yayin da ƙungiyar ke ƙoƙarin ƙarfafa ƴanwasan bayanta a bazara. (Fabrizio Romano)

Arsenal da Chelsea da Liverpool da Newcastle da Spurs sun gana da wakilan ɗanwasan Netherlands Dean Huijsen gabanin yanke shawara kan makomar ɗanwasan Bournemouth mai shekara 19. (Athletic)

Ɗanwasan Belgium da ke takawa Lens ƙwallo Will Still mai shekara 32 yana cikin waɗanda ke neman zama sabon kocin Southampton sakamakon tafiyar Ivan Juric a farkon makon nan. (Talksport)

West Ham na duba yiwuwar ɗaukan mai tsaron ragar Southampton da Ingila Aaron Ramsdale mai shekara 26. (Times)

Real Betis na son fam miliyan 35 yayin da Chelsea ke zawarcin ɗanwasan Sifaniya Jesus Rodrigues mai shekara 19. (Mail)

Newcastle na tsara tayi kan golan Burnley James Trafford mai shekara 22 kuma ta zaƙu ta sayi ɗanwasa Dominic Calvert-Lewin mai shekara 28, yayin da kwantiragin ɗanwasan a Everton zai ƙara a ƙarshen kakar bana. (Football Insider)

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta PSV Eindhoven na zawarcin ɗanwasan Ipswich Jack Clarke mai shekara 24 a wannan bazarar. (Football Insider)

Ana sa ran Atalanta za ta fara karɓar tayin sama da fam miliyan 51 kan tsohon ɗanwasan gaba na Everton Ademola Lookman, 27, yayin da ɗanwasan na Najeriya ke shirin barin kulob ɗin na Italiya a ƙarshen kakar nan. (Calciomercato - in Italian)

Barcelona ta rage kwaɗayinta kan ɗanwasan Bayer Leverkusen Jonathan Tah, 29 wanda kwantiraginsa da kulob ɗin na Bundesliga ya cika ranar 30 ga watan Yuni. (Sport - in Spanish)

Kocin Genoa Patrick Vieira na fafutukar neman zama sabon kocin Roma, yain da tsohon ɗanwasan Arsenal da Faransa ya kasance cikin jerin mutum huɗu da za a zaɓa. (Sky Sport Italia - in Italian)

Daraktan ƙwallon ƙafa na Barcelona Deco ya bayyana ɗanwasan Real Sociedad ɗan Sifaniya Alex Remiro, mai shekara 30, a matsayin wanda zai maye gurbin Marc-Andre ter Stegen na Jamus, mai shekara 32, a matsayin mai tsaron ragar ƙungiyar. (Catalunya Radio via Football Espana)