Lafiya Zinariya: Hatsarin sanya abubuwa a cibiyar sabon jariri

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Lafiya Zinariya: Hatsarin sanya abubuwa a cibiyar sabon jariri
An wallafa

A al'adance a wasu ƙasashe masu tasowa da ke nahiyar Afirka, iyaye mata na yin amfani da wasu abubuwan domin ganin cibiyar jariri ta faɗi da wuri.

Wasu mata a Najeriya da jamhuriyyar Nijar na amfani da turare, gishiri, man goge baki, ƙasa, kashin shanu da sauransu a cibin jariri.

Sai dai likitoci sun ce yin hakan na da matuƙar haɗari ga rayuwar jariri, domin ƙwayoyin cuta za su iya shiga kai tsaye cikin zuciya ko kwakwalwar jariri ta cibiyar.

Shafin intanet na gidauniyar NHS, reshen asibitin jami'ar Milton Kyenes, da ke Birtaniya ya bayyana wasu alamomi da ake ganewa cewa, cibiyar jariri ta kamu da kwayoyin cuta.

Alamomin su ne:

  • Ƙasan cibiyar daidai kan ciki zai sauya launi ya yi ja.
  • Wurin zai kumbura ya yi bororo
  • Idan cibiya na yin jini
  • Tana fitar da wani ruwa kore ko ruwan dorawa mai wari
  • Idan jariri baya karbar ruwan nono ko abinci kamar yadda ya kamata, kuma bashi da kuzari, sannan yana zazzabi.

A cewar asibitin, idan an ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, sai a garzaya da shi ko ita zuwa asibiti.

Latsa makunnin da ke sama domin samun ƙarin bayani daga kwararriyar likitar yara, Dr. Naja'atu Hamza domin jin hanyoyin da ya dace a bi don kulawa da cibiyar sabon jariri.