'Da sana'ar kufta nake fatan haɗa kuɗin aikin larurar laka'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
'Da sana'ar kufta nake fatan haɗa kuɗin aikin larurar laka'
An wallafa

Wata budurwa a Kano ta zama tamkar fassarar salon maganar nan da Hausawa ke cewa "nakasa ba kasawa ba", ta yadda ciwon laka da ta gamu da shi, bai sa ta sallama kanta ga bara da rayuwar ƙasƙanci a titi ba, maimakon haka ta durfafi sana'ar hannu ta aikin kufta don rufa wa kanta asiri.

Maryam Usman Muhammad ta ce ta gamu da larurar laka ce, a wata rana bayan ta dawo daga makaranta.

Bayan ta samu gudunmawa kuma, an yi mata aiki a lakarta karon farko, sai ta koma ba ta iya tafiya da ƙafafuwanta, kai hatta kwanciya da gadon bayanta, Maryam ba ta iyawa.

Likitoci tun a wancan lokaci kuma sun faɗa musu cewa matashiyar ta gamu da larurar ne sanadin cutar tarin TB.

Kuma tana buƙatar a sake yi mata aiki a lakarta, amma saboda rashin kuɗi, ya sa har lokacin da aka ba su a asibiti ya wuce ba a yi aikin ba.

Maryam, jaruma ce wadda ta ce har takan fashe da kuka a baya, idan ta fita ta ga mutane kowa na harkokinsa, amma ita Allah bai ba ta iko ba.

Ta shaida wa BBC cewa ta taɓa yin saurayi a baya, har an yi maganar aure, amma sai wannan ya zo ya lalata maganar gaba ɗaya.

Yanzu dai ta ce ta koyi juriya da ƙarfin zuciya ta yadda ta koyi sana'ar hannu ta sarrafa kufta, da burin wata rana za ta haɗa kuɗin da za ta biya a yi mata aiki har ta samu waraka.

Kafin sannan ta ce za ta koma makaranta don ta ci gaba da karatu, wanda ta hanyarsa take fatan zama 'yar kasuwa.