'Harin Isra'ila ne ya kashe 'yan tagwayena da mahaifiyarsu da kakarsu'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Gianluca Avagnina
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Wasu tagwayen jarirai biyu sun rasa rayukansu a harin da Isra'ila ta kai Zirin Gaza yayin da mahaifinsu ya tafi yi musu rajistar haihuwa.
Kwanan Asser, namiji, da Ayssel mace, huɗu da haihuwa lokacin da mahaifinsu Abu al-Qumsan ya fi karɓo takardun shaidar haihuwarsu a ofishin ƙaramar hukuma.
Bayan ya fita ne maƙwabtansa suka kira shi domin faɗa masa cewa an ragargaza gidansa da ke unguwar Deir al Balah.
Harin ya kuma kashe matarsa da kakar jariran.
"Ban san abin da ya faru ba," a cewarsa. "An faɗa min cewa hari ne ya dira a kan gidan."
Ya ƙara da cewa "ko murnar haihuwarsu ban gama yi ba".
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ƙarƙashin jagorancin Hamas ta ce jarirai 115 aka haifa kuma aka kashe su tun bayan fara yaƙi a zirin.
A cewar kamfanin labarai na AP, iyalan sun bi umarnin ficewa daga gidansu zuwa Birnin Gaza da Isra'ila ta bayar a makonnin farko na yaƙin, inda suka samu mafaka a can.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta nemi jin ta bakin rundunar sojin Isra'ila kan harin, kuma tana jiran amsa.
Isra'ila kan ce tana ƙoƙarin guje wa kisan fararen hula, amma kuma takan ɗora alhakin mutuwarsu kan ƙungiyar Hamas da ta ce suna kai mata hari daga tsakiyar gidajen mutane da kuma ɓuya a cikinsu.
Sai dai ba a fiya jin wata magana kan ɗaiɗaikun hare-hare daga Isra'ilar ba.
An kai wa ire-iren waɗannan matsugunan hari da yawa a 'yan makonnin da suka gabata.
A ranar Asabar, wani harin Isra'ila kan makaranta da ke bai wa Falasɗinawan da suka rasa muhallansu mafaka ya kashe sama da mutum 70, kamar yadda shugaban wani asibiti ya faɗa wa BBC.
Mai magana da yawun sojin Isra'ilar ya ce wai "mayaƙan Hamas da na Islamic Jihad ne ke amfani da makarantar a matsayin mafaka", zargin da Hamas ɗin ta musanta.
Isra'ila ta ce adadin mutanen bai kai haka ba, amma kuma BBC ba za ta iya tabbatar da gaskiyar lamarin ba da kanta.
Mayaƙan Hamas sun kashe kusan mutum 1,200 yayin harin da suka kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023, kuma suka sace wasu 251 zuwa Gaza.
Harin ya haifar da ƙazamin martani daga Isra'ila a kan zirin, wanda ya zama yaƙin da ake yi a yanzu.
A cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza, hare-haren na Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 39,790 tun daga ranar.












