Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Rufa'i Nasir
An haifi Sheikh Ahmad Rufa'i Nasir, a garin Keffi na jihar Nasarawa da ke arewa ta tskiyar Najeriya.
Shehin Malamin ya yi karatunsa na furamare da sakandire a garin na Keffi, sannan ya je makarantar Arabic Teachers College da ke birnin Jos a jihar Plateau, daga nan kuma ya je Jami'ar Jihar Nasarawa, inda ya yi digirinsa na farko da na biyu da ma digirin digirgir, sannan ya je Jami'ar Danfodiyo da ke Sokoto inda ya samu shaidar diploma a fannin malunta.
Sheikh Ahmad Rufa'i Nasir - wanda a yanzu shi ne babban limamin masallacin Juma'a na jami'ar Keffi, ya yi karatu a wajen manyan malaman addini a ciki da wajen Najeriya da suka haɗa da Malam Muhammad Mairawani wanda a wajensa ya yi haddar Al'qur'ani, da marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, da sauran malamai.
Ɗaukar bidiyo: Abba Auwalu
Gyarawa: Umar Isa Ladu



