Foden ya zama gwarzon ɗanƙwallon Premier na ƙungiyar marubuta

An wallafa

'Yan wasan Manchester City Phil Foden da Khadija Shaw sun lashe kyautar gwarazan 'yan ƙwallo ta ƙungiyar marubutan gasar Premier League ta Ingila.

Foden mai shekara 23 ya ci ƙwallo 24 kuma ya bayar aka 10 a wasa 50 da ya buga wa ƙungiyar a dukkan gasa a bana.

Ɗan wasan tsakiyar na Ingila ya samu kashi 42 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a ɓangaren maza, inda ya doke Declan Rice na Arsenal, da kuma abokin wasansa Rodri.

Kyaftin ɗin Arsenal Martin Odegaard, da ɗan wasan gaba na Aston Villa Ollie Watkins, da Cole Palmer na Chelsea, su ne sauran 'yan takarar shida.

Foden ya zama ɗan wasan City na uku da ya ci kyautar cikin shekara huɗu da suka wuce, bayan Erling Haaland a 2023, da Ruben Dias a 2021.

"Na yi matuƙar alfahari da cin kyautar nan," a cewar Foden. "Yanzu zan mayar da hankali wajen gama kakar nan da ƙarfina da kuma taimaka wa City lashe ƙarin kofuna."

City na ƙasan Arsenal a saman teburin Premier, amma tana da kwantan wasa ɗaya yayin da take shirin ɗaukar kofi na huɗu a jere.

Ita kuwa Shaw mai shekara 27, ta zama gwarzuwar 'yar ƙwallo ne bayan ta ci ƙwallo 21 a wasa 18.

'Yar ƙasar Jamaican ta doke Lauren James ta Chelsea, inda Alex Greenwood ta zo ta uku.