Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihin matashi Khaby Lame da ya fi kowa shahara a TikTok
Tauraron, mai amfani da dandalin na sada zumunta na TikTok, Khabane “Khaby” Lame, ya zama mafi shahara a dandalin baki ɗaya.
Matashin, wanda Musulmi ne ɗan ƙasar Senegal, ya zama abin da ya zama ne ba tare da cewa uffan ba, inda har ya zarta fasihiyar mai ƙirƙira 'yar Amurka Charli D’Amelio.
Yanzu haka Lame, mai shekara 22, yana da mabiya miliyan 142.8 a dandalin idan aka kwatanta da D’Amelio mai miliyan 142.3.
Yakan wallafa bidiyon barkwanci a shafinsa, yana mai kwaikwayo tare da nuna yadda mutane ke tsauwalawa kan abubuwa ba tare da wani dalili ba.
Ko mene ne tarihin matashin da aka fi yayi a yanzu?
Ya fara TikTok bayan korona ta raba shi da aikinsa
Khaby ya buɗe shafinsa na TikTok a watan Maris na 2020 yayin da annobar korona ke tsaka bayan ya rasa aikinsa a wata ma'aikata a Italiya.
A watan Nuwamban 2020, D’Amelio ta zama mai amfani da TikTok da ke da mabiya fiye da miliyan 100.
An haifi Khabane “Khaby” Lame a Senegal a shekarar 2000, kuma ya koma garin Chivasso da ke arewacin Italiya yana ɗan shekara ɗaya da haihuwa.
Khaby ya koma gida Senegal yayin da annobar korona ke kan ƙololuwarta a Italiya bayan an sallame shi daga aiki.
"A lokacin annobar tana farko-farko kuma ina zaune ba abin da nake yi, kawai sai na fara yin bidiyo a TikTok," kamar yadda ya faɗa wa mujallar Forbes.
Ana iya siffanta bidiyon da Kharby ke yi da cewa na shaguɓe ne da barkwanci kan yadda mutane ke ɗaukar abubuwa da zafi a ayyukan yau da kullum na rayuwa.
Ɗaya daga cikin shahararrun bidiyonsa shi ne na wani ɗan sanda da ke ƙoƙarin buɗe wata ƙofa ta hanyar yin tsalle tare da dukan ƙofar da ƙafarsa. Sai aka nuno Kharby inda shi kuma ya sa hannu cikin sauƙi ya buɗe ƙofar, yana mai nuni da cewa za a iya buɗewa a sauƙaƙe ba tare da zafafawa ba.
Tun daga sanda Kharby ya fara harkokin nan a Maris na 2020, ya yi haɗaka da manyan taurari a duniya daga fanni da dama. Ƙalilan daga cikinsu akwai ɗan ƙwallo Zlatan Ibramovic, da J Balvin, da Usain Bolt.
Kazalika, an sha ganin sa da 'yan wasan ƙwallon ƙafa a bidiyo kamar Lionel Messi da Kylian Mbappe na PSG.
'Dalilin da ya sa ba na magana a bidiyona'
Abin birgewa da bidiyon Kharby shi ne, yana yin duk waɗannan abubuwa ne ba tare da ya ce uffan ba.
Wannan dalilin ne ya sa mafi yawan mabiyansa ba su ma san harsuna da yake iya magana da su ba.
Yayin hirarsa da mujallar Forbes, Kharby ya bayyana cewa saƙon da yake son isarwa zai fi shiga idan bai yi magana ba fiye da idan ya yi da turancin Ingilishi.
"Ina ganin dalilin da ya sa ba na magana ya fi saurin isar da saƙon - mutane da yawa za su fi gane saƙon fiye da idan na yi magana da turancin Ingilishi. Ina magana ne da harshen duniya, wanda kowa da kowa zai fahimta."
Ya ƙara da cewa yana yawan karaɗe shafukan zumunta don neman maudu'ai.
"Akasarin maudu'an da nake yin bidiyo a kansu ina samun su ne daga harkokin rayuwata na yau da kullum.
"Ina shafe aƙalla awa uku a kowace rana wajen neman maudu'ai. Sai dai ba abu ne mai sauƙi ba kwatakwata. A kodayaushe ina ƙoƙari kar na ɓata wa wani rai, kuma kodayaushe na fi son na yi barkwanci kan ƙananan abubuwa."
'Burina na zama ɗan fim a Amurka'
Da aka tambayi Kharby babban abin da ya sa a gaba, sai ya ba da amsa da cewa fim ɗin barkwanci yake so ya dinga a Amurka.
"Burina shi ne na koma Amurka don na shiga fina-finai. Burina shi na zama ɗan wasan barkwanci, na dinga yin fim da gwanina Will Smith. Daga nan ma ba abin mamaki ba ne na lashe kyautar Oscar!."
Ya ƙara da cewa yana da burin ya mayar da kamfaninsa mai suna Iron Corporation lamba ɗaya a duniya.
"A yanzu dai ina ci gaba da nazari da mayar da hankali kan ayyukana, kuma ba zan karaya ba."