Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asibitin Alabama ya dakatar da haihuwa ta hanyar IVF
Babban asibitin jihar Alabama da ke Amurka ya dakatar da shirinsa na taimaka wa masu neman haihuwa ta hanyar hada kwan mace da maniyyin namiji da aka fisani da IVF a turance.
Hakan na zuwa ne bayan da kotun koli a jihar ta yanke hukuncin cewa za a iya daukar dan tayin a matsayin karamin yaro.
Mahukuntan asibitin sun ce sun damu da cewa marasa lafiya ko likitocin asibitin za su iya fuskantar tuhuma sakamakon hukuncin kotun kolin.
Asibitin ya ce ya ɗauki matakin ne saboda kauce wa yanayin da zai sa likitoci ko marasa lafiya su faɗa tarkon fuskantar shari’a.
A hukuncin da kotunta yanke cikin makon da ya gabata, ta ce doka tana amincewa da matsayin dan'adam ne daga ranar da aka dauki cikin mutum.
Kungiyar masu rajin samun haihuwa da hanyar hada kwan halitta ta IVF, ta ce wannan hukuncin zai hana wasu asibitoci da dama a sassan Amurka gudanar da wannan aikin ga masu bukata.
Kungiyar ta kuma koka kan halin da masu bukatar aikin za su shiga a sassan Amurka.
Jihar ta Alabama kamar sauran jihohin Amurka da dama a kudancin kasar sun haramta zubar da ciki.
A lokacin da kotun kolin kasar ta haramta 'yancin zubar da ciki a 2022, ta bai wa sauran jihohin kasar damar yin dokokinsu kan batun.
Tun bayan matakin ne kuma jihohin da ke karkashin Jam'iyyar Dimokrats suka rika fadada 'yancin, yayin da jihohin da ke karkashin jam'iyyar Republican suka takaita 'yancin.
Mene ne IVF?
'Invitro fertilisation' IVF wata hanyar ce da ke bai wa matan da ba sa iya daukar ciki damar magance matsalolinsu.
Kusan kashi 2 cikin dari na cikin da ake dauka a duniya, ana samunsa ne ta hanyar IVF, kamar yadda hukumar takaita yaduwar cutuka ta Amurka ta bayyana.
Yadda ake yi shi ne akan dauki kwan mace a hada da maniyyin namiji, sannan a saka cikin kwalba domin su kyankyashe junansu a dakin gwaje-gwaje.
Daga nan sai a rika kula da dan tayin a cikin kwalbar har zuwa wani kayyadajjen lokaci kafin a mayar da shi cikin mahaifar matar domin ci gaba da rayuwa.
To sai dai hanyar ba ta da tabbataci, domin kuwa akan sha gwadawa ba tare da an kyankyashe kwayayen ba.
A wasu lokuta kuma akan daskarar da 'yan tayin sannan a ajiye su cikin kwalabe cikin sinadarin nitrogen, inda masana suka ce ana ajiye su na kusan shekara 10.