El Clasico: Real Madrid za ta kara da Barcelona a Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fafata da Barcelona a wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Alhamis.
Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a tsakaninsu a bana, bayan da Real ta ci Barcelona 3-1 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu ranar 16 ga watan Oktoba.
Sai dai Barca ta doke Real 3-1 ranar 15 ga watan Janairu ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia.
Barcelona za ta buga wasan, bayan da Manchester United ta fitar da ita daga Europa League da cin 4-3 gida da waje.
Haka kuma kungiyar Nou Camp ta yi rashin nasara a hannun Almeria a La Liga a karshen mako, karo na biyu da ta yi rashin nasara a gasar a kakar nan.
Ita kuwa Real Madrid ta tashi 1-1 a wasan hamayya da Atletico Madrid a dai fafatawar hamayya a babbbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ce ta daya a teburin La Liga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, Real Madrid 19 ne da ita, wadda ke biye da Athletic Bilbao mai 23.
Labaran da ya shafi kungiyoyin biyu:
Barcelona: Ousmane Dembele da Pedri na jinya, shima Robert Lewandowski ba zai yi wasan ba, daga cikin fitattun 'yan kwallon Barca da ba za su yi karawar ba.
To sai dai Ansu Fati, wanda ya sha jinya, yanzu ya murmure yana cikin wadanda Barca ta ziyarci Real Madrid.
Real Madrid: Har yanzu Ferland Mendy da David Alaba na jinya,, amma dai dan kwallon Brazil, wanda ke taka rawar gani a bana yana cikin 'yan wasan da Real ta bayyana a karawa da Barca.
Dan wasan ya ji rauni a karawar da Real ta ci Liverpool 5-2 a Anfield a wasan farko zagayen 'yan 16 a Champions League.

Asalin hoton, Real Madrid FC
'Yan wasan da Real za su fuskanci Barca:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin and Luis López
Masu ttsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da D. Ceballos.
Masu cin kwallo: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano da Álvaro.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











